Karamar Sallah: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Kwana 2

- Advertisement -

Karamar Sallah: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Kwana 2

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun Laraba da Alhamis, wato 12 da 13 ga watan Mayu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka inda ya yi wa Musulmi murnar kammala azumi da kuma zagayowar ranar Sallah karama.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro su kara jajircewa da zama masu kishin kasa don kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da su a kasar.

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a shirye ta ke ta kawo karshen masu aikata manyan laifuka kuma za ta kawo zaman lafiya mai dorewa a duk wani lungu da sakon a kasar nan.

- Advertisement -