Karamar Hukumar Faskari Ta Kusa Zama Kufai

- Advertisement -

Karamar Hukumar Faskari Ta Kusa Zama Kufai

Daga Awwal Jibril ‘Yankara,

Har yanzu tsuguni ba ta kare ba, kan lamarin tsaro a jihar Katsina ba, musamman a karamar hukumar Faskari.

Kusan kullun sai an samu labarin garuruwan da ‘yan bindida suka shiga suka Kashe mutane, ko suka kwashe su domin neman kudin fansa ko suka kore dabbobin da suka mallaka.

Garuruwa na baya-bayan nan da ‘yan bindigar suka je solar hada kauyan ‘Yantuwaru da Unguwar Goga da Unguwar Sani Mai takalmi da ke kusa da garin ‘Yankara, inda suka yi gaba da mutum kusan 100, ba fi yawa mata, daga bisani solar nemi a ba su Naira Miliyan 100, a wadan nan garuruwan uku kacal, sai  bayan an cim ma yarjejeniya, an biya su, kana suka sako su.

‘Yan bindigar solar je wasu garuruwa da suka hada da Unguwar Gizo da Unguwar Biri da Fankama da ‘Yar Itace da Tsuru da Mangorori da sauransu, inda suka kore daruruwan shanu da tumakai.

‘Yan bindigar a wannan dan tsakanin solar kashe mutane fiye da 30 a wannan yankin na karamar hukumar Faskari.

Haka al’amarin suke a garin ‘Yankara ta karamar hukumar Faskari, wanda zuwa yanzu Kuma kusan kullum sai ‘Yan bindiga solar shiga garin solar dauki mutane domin neman kudin fansa, zuwa yanzu akwai a kalla mata sama da 20 a hannunsu duk ‘yan garin na ‘Yankara, ban da dauki dai-dai a bakin gari ga duk wani da sukai kicibis da shi, ko zai je gewayan gona ko zai je wani kauye da ke cikin lungu, sai dai wanda Allah ya tsare.

Sannan wani Abin bakin ciki shi ne, wani lokaci ko an biya kudin fansa sai su ki sakin mutu, sai su kashe shi bayan biyan kudin fansar.

Haka suka yi kan Malam Yusuf Atoke Mai Yashi, sai da aka biya Kudi Naira Miliyan biyu, suka karbe kudin sannan suka kashe Shi.

Haka Malam Bara’u Mai Fenti da kanensa, sau biyu ana kai kudin fansar amman sama da maki uku ke nan shiru, kusan garuruwan da ke bakin hanya suma solar fara tashi don tsira da rayuwarsu.

A kwanaki biyu a jere, ‘yan bindigar solar kai hari kauyukan Unguwar Sani da Kuceri da ke Mazabar Bilbis a karamar hukumar Tsafe, ta jihar Zamfara da kuma Hayin gada Bilbis a Mazabar Faskari a karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, inda suka tafi da    da mutane da dabbabo.

Haka nan solar je Mai-mai a kauyukan Bilbis inda suka kashe ‘yan banga hudu da

Unguwar Hayaki a Mazabar Sheme a karamar hukumar Faskari.

Wannan na faruwa ne duk da dimbun jami’an tsaron da aka jibge a sansanin soja na Faskari da ‘Yan Sandan kwantar da tarzoma.

- Advertisement -