Kanun Labarai: Daga Litinin 21 Zuwa 24 Ga Watan Ramadan 1442

- Advertisement -

Kanun Labarai: Daga Litinin 21 Zuwa 24 Ga Watan Ramadan 1442

LITININ

Yau ma rana ce ta hutu ta ranar ma’aikata. Saboda ranar ta ɗaya ga wata ta faɗo shekaranjiya Asabar wacce kuma da ma ba aiki, shi ne aka matso da hutun yau Litinin.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin ci gaba da kare muradun aikin jarida, tare da yin kira ga ‘yan jarida su dinga mutunta ƙa’idojin aikin nasu.
kungiyar Kare Hakkin Jama’a da Bunƙasa Tattalin Arziki SERAP a taƙaice, ta kai Gwamnatin Tarayya ƙara gaban kotun ECOWAS, ta yammacin Afirka, a kan wata ƙa’idar hukumar gidajen rediyo da talabijin NBC ta ƙasa, da ke takura wa walwala da ‘yan Nijeriya ke da ita wajen faɗin albarkacin bakinsu a kafofin watsa labaru.
Hukumar tsaro ta DSS/SSS ta gargaɗi masu kalamai musamman na tunzura jama’a kamar yadda wasu malamai da ‘yan siyasa ke yi, da hawainiyarsu ta kiyayi ramarta.
Gwamnatin Tarayya ta hana fasinjojin ƙasashen Birazil, da Indiya da Turkiyya zuwa ƙasar nan saboda yadda ainihin kwaronabairos ta gaskiyar ta addabi ƙasashen. In kuma ‘yan Nijeriya ne ko masu izinin zama a ƙasar nan, suka fito daga can, dole sai an killace su tukuna ta kwana bakwai.
Wasu kidinafas solar kashe kwamishinan al’amuran ‘yan fansho na jihar Kogi, suka yi kidinafin wani shugaban ƙaramar hukuma da wasu.
An kama wasu a lokacin da suke ƙoƙarin satar shanu guda 300 a jihar Zamfara.
‘Yan sanda solar kama wasu mutum shida a Abuja da suke zargin ‘yan fashi ne.
Malaman kwalejojin foliteknik na ci gaba da yajin aiki, bayan solar haura shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, da sauran wasu abubuwa, alhali an daɗe da biyan sauran ma’aikata solar manta solar cinye.

TALATA

Yau ma’aikata ke komawa aiki bayan hutun da suka sha na ranar ma’aikata. Haka nan jiya ta kasance ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya bakidaya.
Yau Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai ci gaba da taro da mataimakinsa da sauran manyan muƙarraban ƙasar nan musamman waɗanda suka shafi tsaro, don ganin yadda za a yi wa matsalar tsaron taron dangi.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince a kafa wata cibiya da za ta yaƙi yawaitar ƙananan makamai da cinikinsu da ire-irensu a tsakanin jama’a.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana sa ran nan da mako biyu, a dawowa da Nijeriya wata yuro miliyan huɗu da ‘yan kai, kwatankwacin Naira Biliyan 22, da Ibori tsohon gwamnan jihar Delta ya sata, ya kai Ingila ya ɓoye.
Hukumar NDLEA ta Buba Marwa da ke sanya kafar wando guda da fataken miyagun ƙwayoyi, ta kai mamaya wuraren yin abinci da ire-irensu da ke Filato da Inugu, ta kuma yi sa’a ta kama koken, da abinci da aka masa haɗi da miyagun ƙwayoyi. Haka nan hukumar ta kama wani saurayi mai shekara 24 da ke sayar da miyagun ƙwayoyi a harabar jami’arsu da yake karatu.
Sojojin haɗin kai da ke yaƙi da Boko Haram, solar daƙile yunƙuri daban-daban da ƙungiyar Boko Haram ta yi don kai hari al’umomi da ke jihar Barno.
‘Yan Nijeriya su fiye da 500 da ke Ghana aka ce an tsare a can, a ci gaba da zargin musgunawa ‘yan Nijeriya da ke zaune a can suna neman halaliyarsu.
Kidinafas da suka yi kidinafin ɗaliban jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna, solar ba gwamnati da iyayen ɗalibai 17 da suka yi saura a hannunsu sa’a 24, ko a ba su naira miliyan ɗari da babura goma su saƙo su, ko su kashe su. Da ma solar kashe biyu da farko, suka ƙara kashe uku suka zama biyar. An tara musu naira miliyan 55 an kai musu, solar ce kuɗin ciyar da ɗaliban ne, saura kuɗin fansarsu.
Kidinafas da suka yi kidinafin shugaban ƙaramar hukuma a jihar Kogi, solar yi masa kuɗi naira miliyan ɗari.
‘Yan sandan jihar Kaduna, na ci gaba da damko wadanda ke da hannu a kidinafin yaron nan ƙarami, suka kuma kashe shi bayan solar masa kuɗi an biya su, tsoron ya gane su, zai kuma tona musu asiri.
A jihar Binuwai wasu mahara solar kashe mutum goma sha uku.
A jihar Kwara an kama wani mai shekara 24 da ƙoƙon kai, da ya ce shi ya kashe mai kan, don ya yi tsafi da shi.
Malaman kwalejojin foliteknik, na ci gaba da yajin aiki saboda ariyas rututu da suke bi, da sauran wasu buƙatu nasu.

LARABA

Jiya Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da taron da suka somo makon jiya da dukkan muƙarraban gwamnatinsa da jiga-jigan da tsaron ƙasar nan ya shafa. Sai bayanan da ke nuna shugabannin sojoji na gargaɗi a kan ‘yan siyasan da ke kokarin zuga wasu sojoji su ƙwace mulki. Hukumomin soja solar ce ba za su lamunta ba
Gobe Alhamis idan Allah Ya kai mu Majalisar Dattawa za ta gana da manyan hafsoshin tsaron ƙaaar nan.
Sanata Ndume ya ankarar cewa ‘yan Boko Haram na nan suna ƙoƙarin sake haɗuwa a yankin Arewa Maso Gabashin Ƙasar nan.
Mutanen Gaidam solar tsere gudun hijira ƙananan hukumomi four da ke jihar Bauci, saboda matsa musu da ‘yan Boko Haram suke ta yi.
Iyayen ɗaliban da kidinafas suka yi kidinafin a makarantar Afaka da ke jjhar Kaduna, solar yi tattaki da takakkiya zuwa Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ke Abuja, don nuna ba su ji daɗin yadda gwamnati ta ƙi yin wani abu a kan ‘ya’yansu da suka kwana biyu a hannun kidinafas ba.
Kidinafas da suka yi kidinafin ɗaliban jami’ar Greenfield da ke Kaduna, da suka ba da wa’adin sa’a 24, ko a fanshi ɗaliban ko su kashe sauran da ke hannunsu, solar saƙo ɗaya jiya. Sai dai iyayen wanda aka sako solar yi gum a kan ko nawa suka biya. Da ma kidinafas ɗin solar kashe biyar daga cikin ɗaliban.
‘Yan bindiga solar kashe mutum biyu da ji wa mutum shida rauni a ƙananan hukumomin Chikun da Kajuru da ke jihar Kaduna.
Minstan sadarwa Pantami, ya ƙara wa’adin zuwa a yi rajistar shaiɗar ɗan kasa, da haɗe lambar shaidar da layin waya, har sai zuwa ƙarshen watan gobe. Karo na biyar ke nan ana ƙara wa’adin.
Hukumar Hisba ta Kano, ta kori wani jami’inta da ake zargin an kama shi da matar aure a otel. Shi kuma ya ce yaji ta yi, ya bi ta ya ba ta haƙuri ta koma gidan mijinta.
Malaman kwalejojin foliteknik na ci gaba da yajin aiki, a kan ariyas da suke bi rututu, da kuma wasu buƙatu nasu.
Bayanai na nuna ministar kuɗi na bayanin za a duba albashin ma’aikata, don ganin yadda za a mayar da shi ta yadda gwamnati za ta iya biya.

ALHAMIS

Iyaye da ‘yan uwan ɗaliban makarantar koyar da alkinta gandun daji ta gwamnatin tarayya da ke Afaka a Kaduna, suna nan jiya murna har kunne, domin kuwa, kamar yadda bayanai suka nuna, Dafta Gumi, da Obasanjo solar yi ruwa solar yi tsaki, kidinafas solar sako su, bayan solar kwashe kwana 57 a hannunsu. Da ma shekaranjiya iyayen ɗaliban suka je Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ke Abuja, suka yi zanga-zanga ta nuna ɓacin ransu a kan yadda gwamnati ta ƙi yin komai a kai. Ɗaliban su 29 da aka sako jiya an ce ta can wuraren Giwa ta jihar Kaduna aka sako su, zuwa yanzun ba a san nawa aka biya don sako su ba, ko ba a biya ko ƙwandala ba.
Sauran ɗaliban jami’ar Greenfiled da ke Kaduna, da waɗanda suka yi kidinafin ɗin suke barazanar za su kashe su, in ba a biya su kuɗin da suka buƙata ba. Solar kashe biyar zuwa yanzun, solar sako ɗaya shekaranjiya.
A yau Majalisar Dattawa za ta yi taro da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan, har da babban shugaban ‘yan sandan Nijeriya, a kan matsalar tsaro.
Majalisar Wakilai ta nemi gwamnatin tarayya, ta tsahirta da batun gudanar da ƙidaya ta kasa da za a yi a shekarar nan, har sai an magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar nan a halin yanzun.
Sojoji solar ceto mutum 13, sannan ‘yan bindiga solar kashe mutum biyu a yankin ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
Gwamnatin jihar Katsina na shirin mayar da almajirai su duba bakwai jihohinsu.
Malaman kwalejojin foliteknik na ci gaba da yajin aiki a kan ariyas da suke bi rututu, da sauran wasu buƙatu nasu.
Na leƙa inda ake rabon alƙaluman kwaronabairos ban ga sabbin alƙaluma ba.
Ana ci gaba da yin kira ga gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ɗan dinga taka-tsantsan da irin ɓarin zancen da yake yi.

- Advertisement -