Kansiloli 7 Cikin 11 Sun Dakatar Da Shugaban karamar Hukumar Chanchaga

0
95

Kansiloli 7 Cikin 11 Sun Dakatar Da Shugaban karamar Hukumar Chanchaga

A daidai lokacin da ake tataburza a karamar hukumar Shiroro kan dakatarwar da kansiloli su kaiwa shugaban karamar hukumar, Hon. Sulaiman Chukuba kan zargin almundahana da ruf da ciki da kudaden gwamnati, wanda zuwa yanzu an kasa samu bakin zaren duk da yunkurin masu ruwa da tsaki a karamar hukumar da majalisar dokokin jihar da ya janyo gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello kafa kwamiti dan yin bincike akan korafe korafen kansiloli.

karamar hukumar Chanchaga ma ba ta tsallake irin wannan tarkon ba, inda a talatar makon nan kansilolin karamar hukumar bakwai cikin sha daya suka dakatar da shugaban karamar hukumar, Hon. Ibrahim Abubakar Lalalo da mataimakinsa, Hon. Salisu Sa’idu tsawon watanni uku.

Shugaban karamar hukumar wanda shi ne shugaban kungiyar shugabannin kanananan hukumomin jihar (ALGON), photo voltaic zarge shi ne da rashin gudanar da mulki bisa ka’ida da rashin bayyanawa kansilolin yadda yake kashe kudaden da ke shigowa aljihun karamar hukumar.

Yadda Ta Kaya A Zaben kananan Hukumomin Jihar Bauchi

Wani kansulan da ya nemi a sakaya sunan sa, yace shugaban karamar hukumar bai zama ofis, mu a matsayin mu na kansilolin da ya kamata yana aiki tare da mu kafada da kafada tun da zaben mu aka yi kamar yadda aka zabe shi ba mu san yadda ake gudanar da mulkin karamar hukumar nan ba.

Yanzu da yawan mu kansiloli ba ma iya shiga cikin jama’a, dan ba mu da abin ce masu, yau mun kwashe shekara daya da watanni a majalisar karamar hukumar nan amma ba wani kansulan da zai iya daga yatsa ya nuna wani abinda zai bari da ya kawo wa mazabarsa, wanda mun sha nunawa shugaban amma bai saurare mu ba.

Kansilolin photo voltaic ce kundin tsarin mulkin kasar nan da ya samar da majalisun kananan hukumomi ya tsara yadda aiki zai tafi kafada da kafada tsakanin kansiloli da zababben shugaban karamar hukuma. Amma mu a karamar hukumar Chanchaga an sakarwa mataimakin shugaban karamar hukumar zaman dumama kujera bai da karfin zartas da duk wani abin da ya dace.

A takardar sanarwar da tawagar kansilolin suka fitar ranar talata photo voltaic bayyana cewar kamar yadda doka ta tanadar idan aka samu irin wannan yanayin, shugaban majalisar kansiloli ko mai tsawatarwa ne zasu cigaba da jan ragamar majalisar karamar hukuma kafin kammala wa’adin dakatarwar idan an cin ma daidaito.

Zuwa yanzu dai akwai majalisun kananan hukumomi da dama a jihar Neja da ake nunawa juna yatsa tsakanin kansiloli da shugabannin kananan hukumomin kan yadda ake tafiyar da harkokin mulki a wasu yankunan kananan hukumomin.

Jama’a dai photo voltaic zura ido dan ganin irin matakan da majalisar dokokin jihar za ta dauka kan wannan lamarin da har yanzu an kasa shawo matsalar karamar hukumar Shiroro sannan ga na karamar hukumar Chanchaga duka da wa’adin mulkin shugabannin kananan hukumomin na shekaru biyu na gangarowa.

What's On Your Mind?