Kano Pillars Ta Koma Mataki Na Biyu A Firimiyar Nijeriya

- Advertisement -

Kano Pillars Ta Koma Mataki Na Biyu A Firimiyar Nijeriya

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi nasarar doke Adamawa United da ci 1-Zero a wasan mako na 21 da suka kara ranar Lahadi a wasan gasar firiya ta kasa kuma wasa na biyu tun komawa zangon wasa na biyu.

Pillars wadda ke buga wasanninta na gida a jihar Kaduna ta zura kwallo a raga ne ta hannun kyaftin, Rabi’u Ali, kuma sauran minti 10 a tashi daga fafatawar sannan da wannan sakamakon Pillars ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburi da maki 40 iri daya da na Akwa United wadda take ta daya, bayan da ta ci Dakkada 2-Zero.

Jumullar wasa tara aka buga a karawa ta 21 a gasar Firimiyar Najeriya ranar Lahadi, wadda aka ci kwallo 13, sannan kungiyoyi hudu suka ci wasa a waje sannan Ribers United ta je ta doke Rangers 1-Zero, Akwa United ta dura biyu a ragar Dakkada, Mountain of Hearth ma ta ci 2-Zero a gidan Warri Wolbes da wanda Nasarawa United ta je ta doke Wikki da ci 2-1.

Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin gida har hudu da suka sha kashi tun bayan mako na 15 a bara da aka yi irin wannan bajintar  a kakar wasa ta bana da ake bugawa ta wannan shekarar.

Dan wasa Ahmad Musa, wanda ya fara bugawa kungiyar wasa a wannan satin shine ya zama kaftin din kungiyar kuma ya buga wasa mai kayatarwa duk da cew bai zuwa kwallo a raga ba a fafatawar.

Sakamakon wasannin mako na 21 a gasar Firimiyar Najeriya:

Rangers Zero-1 Rivers Utd

Dakkada Zero-2 Akwa Utd

Wikki 1-2 Nasarawa Utd

Warri Wolves Zero-2 MFM FC

Sunshine Stars Zero-Zero Jigawa GS

Kano Pillars 1-Zero Adamawa Utd

Heartland 2-Zero Katsina Utd

Kwara Utd 2-Zero Plateau Utd

Lobi 2-Zero FC Ifeanyi ubah.

 

- Advertisement -