Kano: Budurwa Ta aike wa saurayinta ƴan fashi

0
37

Kotun majistiri mai lamba 18 da ke gyaɗi-gyaɗi a Kano ta ƙi amincewa da bada belin budurwar da ta aika wa saurayinta ƴan fashi.

A zaman kotun na ranar Alhamis mai shari’a Auwal Yusuf Sulaiman yayi watsi da buƙatar lauyoyinta inda suka nemi a bada belinta da matasan da ake zargin ta aika don afka wa saurayinta.

Tsohuwar Matar Adam A Zango ta Mayarwa Da Adam a zango Martani Mai zafi Da Ya dauki Yan kallo

Kamr yadda Freedom radio na ruwaito a kwanakin baya ne aka zargi budurwar mai suna Fatima Umar mazauniyar Ɗantsinke da ke ƙaramar hukumar Kumbotso da aika wa saurayinta gungun wasu matasa 6 har gida ɗauke da makamai saboda ya daina son ta.

What's On Your Mind?