Kananan Ma’aikata 2000 Za Su Samu Gidajen Gwamnati A Jihar Nasarawa

- Advertisement -

Kananan Ma’aikata 2000 Za Su Samu Gidajen Gwamnati A Jihar Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya na samar da gidaje 2000 ga masu karamin karfi a jihar.

Yarjejeniyar wacce ta samu hadin giwar Gwamnatin jihar Nasarawa, da Bankin Mortgage da kuma Gidauniyar Gidajen Iyali, wanda aka shirya don samar da gidaje 2000 ga masu karamin karfi da kuma masu hada-hadar kudade da ake bukata don mutane su sayi gidaje akan farashin mai rahusa.

Da yake jawabi Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana wannan hadin giwar a matsayin Babban cigaba wanda yayi dai dai da manufofin gwamnatin jihar.
A cewar Gwamnan, sanya hannu kan yarjejeniyar, zai samar da tattalin arziki da bunkasa ayyukanyi a jihar, tare da samar da gidaje ga masu karamin karfi, masamman ma’aikata da ke karbar kasa da N100, 000 a wata.

Gwamna Sule ya jinjina wa FMBN saboda hadin gwiwa da Gidauniyar Gidajen Iyali, sannan kuma ya yi godiya ta musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari, kan kirkirar wannan tunanin, da nufin tabbatar da cewa marasa karfi daga cikin al’umma solar mallaki gidaje, don magance matsalolin rayuwa da gidaje.

Gwamnan ya cewa a yayin gudanar da wannan aikin al’umman jihar Nasarawa, dama zasu samu ayyukan yi
“Idan kimanin mutum 20,000 daga cikin wadanda suka kammala karatun mu wadanda ke yawo a titunan jihar za su samu ayyukanyi lokacin wannan aikin. Wannan shi ne babban abin da yake karfafa min gwiwa,”
Gwamnan ya kara da cewa Gwamnatinsa na sane da cewa, wannan tsarin na mallakar filaye a kusa da Babban Birnin Tarayya, Jihar Nasarawa ta kasance jihar dake sahun gaba idan ana batun mallakar fili.

Gwamnan ya ce ya ba da shawarar ne don ciyar da jihar gaba, don ganin abin da zai zo jihar ya zama amfanin dukkan abokan hadin gwiwa.

Abdullahi Sule ya ba da tabbacin cewa Gwamnatinsa za ta sa ido sosai kan aikin, don tabbatar da cewa an aiwatar da shi kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

Shima da yake jawabi, Manajan Daraktan Asusun Gidaje na Iyali, Femi Adewole, ya bayyana sanya hannu kan yarjejeniyar a matsayin wani babban abin tarihi, tare da kamfaninsa ya bayar da zunzurutun naira biliyon shida (N6b). wajen aiwatar da aikin.

Adewole ya bayyana cewa aikin zai kasance tare da wasu, gina gidaje 2000, gami da hada-hadar kudade da ake bukata don mutane su sayi gidajensu.

Adewole ya kuma bayar da tabbacin cewa kayayyakin da za a yi amfani da su wajen ginin za a samu su a cikin gida.
Ya bayyana sanya hannu kan yarjejeniyar, wanda kuma aikin gwaji ne, a matsayin sabon salon samar da gidaje, ta hanyar kawo dukkanin abubuwa masu mahimmancin ƙimar gidajen a ƙarƙashin rufin ɗaya.

“Wannan zai kawo karshen gazawar da ke addabar ayyukan gidaje a Najeriya. Wannan ita ce mafita wacce ba kawai za ta kawo wa jihar Nasarawa suna ba, amma muna sa ran amfani da wannan nasarar a Nasarawa, don yin kwazo a fadin jihohi da dama.

Shima Manajan Daraktan Bankin Bayar da Jinginan Tarayya, Arch. Ahmed Musa Dangiwa, ya ce yarjejeniyar ta bangarorin uku za ta daukaka matsayin hadin kai da kawance da bankin da kuma jihar Nasarawa.

Babban bankin na FCMB, wanda Oladapo Fakeye, Shugaban kungiyar dabarun, ya wakilta a wajen taron, ya bayyana cewa bankin ne ke kula da Asusun Gidauniyar Tarayya.

- Advertisement -