Kamfanonin Kasar Amurka 3500 Sun Ki Yarda Da Karbar Karin Haraji Kan Kayayyakin Kasar Sin

Wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gabatar a jiya Asabar, ya ce, cikin makonni 2 da suka wuce, kamfanonin kasar Amurka kimanin 3500 photo voltaic shigar da kara a kotu, bisa zargin matakin da gwamnatin shugaba Trump ta dauka, na karbar karin haraji kan kayayyakin kirar kasar Sin, wadanda darajarsu ta zarce dalar Amurka biliyan 300, da cewa ya saba doka.

Kamfanonin Kasar Amurka 3500 Sun Ki Yarda Da Karbar Karin Haraji Kan Kayayyakin Kasar Sin

Wadannan kamfanonin photo voltaic hada da Volvo dake samar da manyan motoci, da kamfanin Pep Boys mai hada kayayyakin mota, da kamfanin Ralph Lauren mai samar da tufafi, da dai sauransu.

Cikin kararrakin da suka shigar a kotun dake kula da batun cinikin kasa da kasa ta kasar Amurka, suna zargin wasu jami’ai da hukumomin kasar Amurka da yunkurin ta da rikici ta fuskar ciniki, tsakanin kasashen Amurka da Sin. (Bello Wang)

 242 total views,  3 views today

About M. Jamiu 1057 Articles
Muhammed Jamiu is a Head Editor at Mobilized9ja (M9JA). He has been publishing for 8 years and focused more on Local/World News, Nigeria Music & Video all in English and Hausa Language.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*