Kalli yadda dakarun sojin Nigeria suka lallasa Boko Haram da ISWAP (bidiyo)

0
27

A wani lamari da ya zai faranta ran yan Najeriya da dama, rundunar sojojin kasar ta yi gagarumin nasara ta hanyar lallasa wasu mambobin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP.

Dakarun solar kuma yi nasarar kwato wani sansanin sojoji daga yan ta’addan a karshen mako.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a ranar Juma’a, 15 ga watan Janairu, yan ta’addan solar kwace Marte, wani gari da ke kilomita 93 daga Maiduguri, babbar birnin jihar Borno, da sansanin sojoji da ke chan.

Sakamakon haka, sai dakarun soji suka kai harin bazata kan tawagar yan ta’addan kafin suka kakkabe su.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga jagoran labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Enenche.

Kalli yadda dakarun sojin Nigeria suka lallasa Boko Haram da ISWAP

Ya ce rundunar sojin sama na Operation lafiya dole ta lalata karin motocin bindiga shida sannan suka shafe yan ta’adda da dama wadanda ke kokarin karfafa takwarorinsu a harin.

Sai dai yan ta’addan na ikirarin wani batu na daban.

Yadda ake bawa ‘yan Boko Haram horaswa irin ta sojoji a sabon bidiyon farfaganda

A cewar wata sanarwa a shafinsu na Amar information a Telegram, ISIL solar yi ikirarin cewa an kashe mutane bakwai, an kuma kama mutum daya.

Yan ta’addan solar kuma yi ikirarin cewa mayakansu solar kwace makamai, alburusai da motoci shida sannan cewa solar kona sansanonin soji.

Babu tabbaci kan wannan ikirari nasu.

A wani labarin, a ranar Lahadi, 17 ga watan Junairu, 2021, rundunar sojojin Operation Hadarin Daji suka kashe ‘yan bindiga 35 a jihar Zamfara inji jaridar Punch.

Rahotanni solar bayyana cewa sojojin kasar solar yi nasarar karbe wasu dabbobi da miyagun suka sace.

Babban jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a Gusau, jihar Zamfara.

What's On Your Mind?