Kalli Hotunan wata gawa da aka yi mata ado aka dinga daukar hotuna da ita ya jawo kace-nace

0
142

Wannnan Ya Faru Da Gaske A Zahiri Ga Rahoton Yadda Abin Ya Wakana Yake.

Hotunan wani mutumi da ya mutu da aka dandasa masa kwalliya ‘yan dangi kowa da kowa yazo ake daukar hoto da shi yana ta faman yaduwa a shafukan sadarwa, inda mutane ke ta cece-kuce a kanshi.

A yadda rahoto ya nuna, mataccen mutumin yana ajiye a dakin ajiye gawa na asibiti fiye da watanni hudu inda aka yi masa ado sosai, dangin shi suke zuwa suna daukar hotuna da shi a yayin da aka tada shi tsaye.

Mamacin a yadda rahotanni suka bayyana sunansa Dr Luke Nkanele, wanda yake daya daga cikin manyan dakarun St Mulumba.

Har yanzu dai ba a tabbatar a wace kasa ne aka dauki wannan hotuna ba a daidai lokacin da aka wallafa rahoton.

Sai dai hotunan solar sanya mutane suna ta kace-nace a shafukan sadarwa.

Ga dai hotunan a kasa:-

:-Ku kasance Tare Damu Akodayaushe Domin Samun Sabbin Labarai.

What's On Your Mind?