Kai Tsaye:- An Shiga Zaman Gaggawa Na Majalisar Zartarwar Jam’iyyar Apc A Aso Rock

0
194


Majalisar zartaswar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yanzu haka na zaman gaggawa a fadar shugaban kasa, Aso Villa, dake birnin tarayya Abuja. Za ku tuna cewa jam’iyyar ta shirya zaman a watan Nuwamba domin sanin abin yi kan shugabancinta amma bata samu dama ba. 

Shugaban kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jagoranci sauran mambobin majalisar zartaswar, har da shugaba Buhari wajen bude taron. 

Sauran wadanda ke hallare a zaman sune shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila. 

Hakazalika gwamnonin jam’iyyar, karkashin jagorancin shugabansu gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu na hallare. 

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita. Karin bayani na nan tafe.

What's On Your Mind?