Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Daliban Jami’ar Greenfield Biyu

0
118

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Daliban Jami’ar Greenfield Biyu

‘Yan bindigar da suka sace daliban jami’ar Greenfield dake Kaduna, solar sake kashe biyu daga cikinsu. Cikin sanarwar da kwamishinan lamurran tsaro Samuel Aruwan ya fitar ya ce an tsinci gawar daliban ne a yau Litinin.

Sanarwar ta ce “Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai tana bakin cikin wannan mummunar aika-aika da aka yi wa daliban da ba su ji ba ba su gani ba da aka sace yayin da suke ci gaba da neman ilimi don samun makoma mai kyau.”

A makon da ya gabata ‘yan bindigar suka kashe uku daga cikin daliban waɗanda ‘yan bindiga suka sace a ranar Tatalar da ta gabata.

What's On Your Mind?