Kabilar Banyakole Da Al’adun Su Na Aure

- Advertisement -

Kabilar Banyakole Da Al’adun Su Na Aure

Daga Muhammad Umar Minna

kabilar Banyakole, kabilace da ke mutun ta ‘yanci diya mace musamman wajen martaba igiyar aure. Bisa al’ada suna ganin ba wani abu da yafi muhimmanci kuma yake kawo kwanciyar hankali kamar zaman lafiya da samun fahimtar ma’aurata.

Inda suka dauki gwajin budurci a matsayin muhimmin abu musamman ga budurwar da aka aurar dan sanin karfin jima’in namiji ta hanyar anfani da gwaggwan amarya.

Hanyar farko da kabilar Banyakole na kasar Uganda itace na hada yarinyar da za a aurar da kanwar mahaifiyarta ta zamo mata babbar kawa, saboda kauna da soyayya da jagorantar ‘yar ‘yar uwarta ta hanyar zama aminiya, musamman akan abubuwan da ba za ta iya rabawa da mahaifiyarta ta hakiki ba.

A wajen kabilar Banyakole aikin gwaggo ya wuce nasiha ko yin fada ba har ma da daukar duk wani nauyi da ya gagari amarya ta al’adance.

Mutanen Banyakole da ake kiransu Ankole mazauna masarautar Bantu ce wadda ta samo asali tun karni na sha biyar. Tana Kudu maso yammacin Uganda, gabas da tafkin Edword masarautar da Mugabe ke mulki, wace ta shahara ga kare hakkin aure na musamman.

Auren Banyakole;
Wannan auren a cikin al’ada yana da muhimmancin gaske, yayin da iyaye kan kasance cikin farin ciki da auren ‘yayansu. A bisa al’adar Banyakole, idan yarinya ta kai shekarun haihuwa takwas zuwa tara aikin gwaggon ta ne ta gyara ta dan rayuwar iyali, za ta koyar da yarinyar duk wani abu da ya kamata ta sani sport da matsayinta na mace mafi muhimmanci a matsayin matar aure.
Budurci a cikin wannan al’adar ana muhimmantar da shi domin ana girmama shi sosai, don haka dole ‘yan mata su kaucewa yin jima’i kafin aure, domin idan aka gano yarinyar ta kau da budurcinta kafin aure za ta fuskanci hukuncin kisa ko yanke mata hukunci daga al’ummarta.
Bugu da kari mutanen Ankole suna daukar wasu matakai na gyara budurcin budurwa, lokacin da yarinya ta kai shekaru takwas zuwa tara ana bukatar su rinkayin kitso inda ake ciyar da su gero, naman shanu da madara. Ana yin wannan ne dan baiwa ‘yan matan damar janyo hankalin mazaje dan yin aure.
Auren su ya kunshi shagulgula da dama ciki har da lokacin bayar da kyauta da aka fi sani da “Kuhingira” inda dangi da abokan amarya kan gabatar mata da kyaututtuka kamar shanu da kayan abinci da zasu kai gidanta na aure. Inda bayan kwanaki goma ina aiwatar da wata al’ada da ake cewa ” Okukoza Omunurori” a nan ne za a sanya amarya ta dora girki ta kunna wutan girki na farko.

A ranar daurin aure, ana shirya buki a gidan amarya inda mahaifinta zai yanka bajimin sa, yayin da a gidan ango akwai wani buki na kara aure. Amma da farko dole ayi bukin gargajiya na karshe, bukin da ya kunshi gwaje-gwaje guda biyu wanda dole ne gwaggwon amarya ta gudanar da su.
Don haka, gwaji na biyu karfin jima’i daga gwaggwon amarya ta hanyar yin jima’i tsakaninta da mijin amaryar. Wannan abin na faruwa ne a gaban amaryar lokacin da angonta ke biyan bukatarsa da gwaggwon ta, wanda tilas ne a gudanar da shi kamar yadda al’ada ta tanada.
Tunda budurci shi ne ma’aunin aure ga matan Banyakole, dole kowace amarya a gwada ta da gwaggwon ta dan tabbatar da budurcinta kafin auren. Idan amarya ta wuce gwajin budurci ana zaton ba ta da ilimin jima’i ko yadda zata farantawa sabon angonta rai ta hanyar saduwa da shi a shinfida.
Gwajin na biyu gwaggwon amarya ce za ta horar da amarya yadda ya kamata ta gamsar da mijinta ta hanyar kwanciya da gwaggwon a gaban amaryar, dan nunawa amaryar dubarun kwanciya da hanyoyin da za ta gamsar da mijinta da shi angon da amaryar a daki daya yayin gwajin da ita gwaggwon amarya.

- Advertisement -