Ka tuba kuma ka Musulunta, Shekau ga sabon shugaban hafsan tsaro

0
49

Shugaban yan ta’addan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon jawabin cewa, babu abinda sabbin hafsoshin tsaron zasu tsinana kamar yadda magabatansu sukayi wajen yaki da ta’addanci a Arewa maso yammacin Najeriya.

Hakazalika Shekau ya yi kira ga sabon shugaban hafsoshin tsaro, Manjo Janar Fortunate Irabor, ya tausayawa kansa, ya tuba kuma ya Musulunta.

Shekau, wanda yayi magana na tsawon mintuna goma, ya yi kira ga sabon shugaban hafsan Sojojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya sani cewa abubuwan da yake yi ya sabawa addinin Musulunci, saboda haka ya kafurta.

Ka tuba kuma ka Musulunta, Shekau ga sabon shugaban hafsan tsaro

A cewar Shekau, zasu kai sabbin hare-hare a kasar, kuma yan Najeriya su daina tunanin sabbin hafsoshin ba zai haifi da mai ido ba.

Mahaifiyar marigayi janar Alkali ta Rasu

Ka tuba kuma ka Musulunta, Shekau ga sabon shugaban hafsan tsaro

Za ku tuna cewa sabon shugaban hafsoshin tsaro, Manjo Janar Fortunate Irabor da sabon shugaban Sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru solar jagoranci yaki da yan ta’addan Boko Haram karkashin atisayen Operation Lafiya Dole.

What's On Your Mind?