Juventus Za Ta Nemi Tikitin Kofin Zakarun Turai A Hannun Inter Milan

- Advertisement -

Juventus Za Ta Nemi Tikitin Kofin Zakarun Turai A Hannun Inter Milan

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan a karkashin jagorancin mai horarwa, Antonio Conte ta samu nasarar  lashe  gasar Seria cin kofin Seria A, sai dai gwagwarmayar wadanda za su samu zuwa gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa ta yi zafi.

Maki uku ne kawai ya raba Atlanta da ke matsayi na biyu da kungiyar kwallon kafa ta Juventus da mataki na biyar 5 kwantn wasanni  biyu kuma kafin a karkare kakar wasan za’a kammala wasannin gaba daya.

Atalanta da AC Milan na da maki 75 kowanne, sai kungiyar Napoli da ke matsayi na hudu na biye da maki 73, sai Juventus da maki 72 a matsayi na 5 sai dai ana iya fayyace wadanda za su samu shiga gasar zakarun Turai na badi a karshen wannan makon.

Idan  Atalanta da Milan suka samu nasara, dukkanninsu za su samu tikitin shiga gasar, saboda su na gaban Juventus a gwabzawar da suka yi a tsakaninsu wanda hakan zai kawo babbar matsala a kungiyar ta Juventus.

Wasanni hudu ne kawai Juventus suka samu nasara daga cikin guda tara da suka buga a baya bayan nan, kuma su na bukatar doke kungiyar Inter Milan domin samun tikitin gasar zakarun Turai.

Idan Juventus suka gaza doke Napoli domin samun ilahirin maki three, zai zame musu dole su koma fafatawa a gasar Europa a kaka mai zuwa wanda hakan ba karamin nakasu bane ga kungiyar  ‘yan wasanta.

‘Yanzu  kociyan kungiyar Andrea Pirlo zai yi fatan dan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a gasar Seria A, wato Cristiano Ronaldo ya taimaka wa tawagar wajen samun nasarar da ake bukata.

- Advertisement -