Juventus Za Ta Iya Rasa Gurbin Zakarun Turai

- Advertisement -

Juventus Za Ta Iya Rasa Gurbin Zakarun Turai

Daga Abba Ibrahim Wada

kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta wargaza lissafin abokiyar hamayyarta kungiyar Juventus dake fatan kammala gasar Seria A ta bana a tsakanin kungiyoyi hudu na farko, bayan fafatawar da suka yi a daren ranar Lahadi.

Ya yin wasan dai AC Milan ta lallasa Juventus ne da kwallaye Three-Zero, ta hannun ‘yan wasanta Brahim Diaz, Fikayo Tomori, da kuma Anton Rebic a fafatawar da sukayi a filin wasa na Turin.

Yanzu haka Juventus ta koma matsayi na 5 da maki 69, maki daya tsakaninta da Napoli dake matsayi na four, yayin da ya rage wasanni Three a buga domin karkare wasannin gasar Seria A na bana.

Sai dai masana na ganin akwai jan aiki gaban Juventus kafin ta sake komawa cikin kungiyoyi four na farko, la’akari da cewar dole ta samu nasara a kan Inter Milan da tuni ta lashe kofin Seria A na bana, yayin karawar da za suyi a karshen mako mai zuwa.

Publicité
Yanzu haka dai kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan da ta dage kofi na da maki 85, Atalanta na biye da ita da maki 72, AC Milan ta Three itama da maki 72, yayin da Napoli ke da maki 70 a matsayi na four.

- Advertisement -