Juna-biyu Ta Yi Kundunbala Cikin Ruwa Don Ceto Mijinta

0
23

Wata mata mai juna biyu ta samu nasarar ceton mijinta daga bakin wani katon kifi a Florida.

A ranar 20 ga watan Satumba ne kifin ya kai wa wani mutumi dake cikin jirgin ruwa hari, wanda a sakamakon ciwukan da ya ji, a yanzu haka yana asibiti rai a hannun Allah. Mutumin yana da mata mai dauke da juna biyu ba yi wata-wata ba ta fada cikin ruwa don ceton ran mijinta lokacin da wannan katon kifi ya kai mishi farmaki a cikin teku.

Juna-biyu Ta Yi Kundunbala Cikin Ruwa Don Ceto Mijinta

Wannan al’amari ya faru ne a ranar Lahadi 20 ga watan Satumba, yadda saura kiris wannan kifi ya aika wannan mutumi mai suan Andrew Eddy, mai shekaru 30 da haihuwa hahira a wannan farmaki, yayin da yake cikin jirgin ruwansa a yankin Sombrero a Florida.

A yadda rahotonni suka nuna, katon kifin ya ciji kafadar mutumin ne, sakamakon haka ya sanya take a wajen jirgin ya kife cikin ruwa.

Karanta: Girmamawa yana Dauke – Kalmomin Girmamawa

Matarsa mai suna Margot Dukes Eddy mai shekaru 29 ta shige ruwan cikin hanzari ta janyo mijinta bayan ta hango yadda jini ya gauraye da ruwan, da kuma wani sashi na jikin kifin. A yadda Christopher Aguanno ya ba da rahoto, ba Eddy da matarsa kadai bane a cikin jirgin ruwan, har da iyayen matar tasa, da kanwarta da kuma saurayin kanwar, wadanda suka fada cikin ruwan lokacin da kifin ya kawo harin.

What's On Your Mind?