Shekara 60 Da ‘Yancin Kan Nijeriya: Jonathan Ya Nemi A Ci Gaba Da Tattauna Batun Daidaito A Kasa

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi kira da a ci gaba da tattaunawa batun kasa don neman adalci da daidaito don ci gaban kasar.

A sakon nasa na murnar samun yancin kai da aka wallafa a shafinsa na twitter, @GEJonathan, tsohon shugaban ya bukaci yan Najeriya da kada su yanke kauna da kasar.

Jonathan Ya Nemi A Ci Gaba Da Tattauna Batun Daidaito A Kasa

Kamar yadda yake ce was: “Ya ku ‘yan Kasa masu kishin kasa, yayin da muke bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai, ya kamata mu gane cewa da yawa ba su samu damar ganin wannan lokacin ba, a yayin da wasu kuma photo voltaic mutu akan aikinsu don kiyaye hadin kan kasarmu da kuma ciyar da ci gaban kasarmu da al’ummarmu gaba. .

Shekara 60 Da ‘Yancin Kan Nijeriya: Atiku Ya Taya Nijeriya Murna

“Ina yabo na musamman ga wadannan masu kishin kasa wadanda za su ci gaba da kasancewa gwarazanmu. Kuma ga dukkan sauran ‘yan Najeriya, wannan ba lokaci ba ne na yanke kauna ga kasarmu.

“Yakamata mu dage da aiyuka nagari; inganta zaman lafiya, hadin kai da kyakkyawan fata. Musamman mu dore da tattaunawa kan batun kasa domin neman daidaito, adalci da hadin kai da ci gaba.

Ina taya mu Murnar Bikin Tunawa da Ranar ‘Yancin Kai!

 289 total views,  3 views today

About M. Jamiu 1102 Articles
Muhammed Jamiu is a Head Editor at Mobilized9ja (M9JA). He has been publishing for 8 years and focused more on Local/World News, Nigeria Music & Video all in English and Hausa Language.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*