Jirgin MaxAir Ya Fara Tashi Da Sauka A Filin Jirgi Na Sir Ahmadu Bello Da Ke  Birnin Kebbi

0
80

Jirgin MaxAir Ya Fara Tashi Da Sauka A Filin Jirgi Na Sir Ahmadu Bello Da Ke  Birnin Kebbi

Daga Umar Faruk Birnin-Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta sa hannu kan yarjejeniya ta fara jigilar fasinjoji da kamfanonin jiragen sama na cikin gida wato Max Air  don fara sufuri a filin jirgin sama na Brinin-Kebbi kan yarjejeniyar fahimtar juna ta MOU da aka sa hannu tsakanin gwamnatin Kebbi da kamfanin.

Jirgin farko ya sauka a filin jirgin saman Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi da misalin karfe 11: 07 na daren jiya dare da fasinjoji da wasu jami’an kamfanin MaxAirline.
Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Kanar Samaila Yombe Dabai mai ritaya ya jagoranci liyafar maraba da ta kunshi manyan ma’aikatan gwamnati tare da kaddamar da fara aikin jirgin zuwa jihar ta kamfanin jirgin sama na Max  Air a Maxadin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu.
Kanar Samaila, Mataimakin Gwamnan wanda ke cike da farin ciki, ya ce, jihar Kebbi na daya daga cikin mafi kyawun hanyoyin da wurare saukar jiragen sama a duniya.
Ya ce an saka wa Filin Jirgin Saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi kyawawan kayan aiki da kuma hanyar sauka.
Mataimakin Gwamnan ya yarda cewa MaxAir ya mallaki ingantattun kayan aiki da jirgin sama gami da kwararrun ma’aikata wadanda za su yi aiki cikin sauki.
Ya umarci kamfanin jirgin sama da ya kiyaye lokaci sannan ya yi addu’ar ga Allah Madaukakin Sarki don samun nasara da aminci ga tashi da sauka.
Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Alhaji Abubakar Chika Ladan yayin da yake maraba da kamfanin jirgin zuwa Kebbi ya ce kamfanin jirgin zai rika bayar da aiyukan jirgin sau uku duk mako tare da fatan fadada wa nan gaba.
A nata bangaren, Gwamnatin Jihar Kebbi za ta bai wa kamfanin jirgin duk wani tallafi da ake bukata ta hanyar hadin gwiwar MOU, in ji shi.
Kwamishinan ya tuna cewa tattaunawa da kamfanin ya faro ne a shekarar 2019, amma aka dakatar da shi a tsakani bayan haka Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya ba da umarnin a ci gaba da tattaunawa da kamfanin jirgin wanda ya bude hanyar sanya hannu kan yarjejeniyar ta MOU tsakanin gwamnatin da kamfanin MaxAir.
A nasa martanin, Dan Babban Shugaban Kamfanin wanda ya wakilci mahaifinsa, Alhaji Dikko Mangal ya gode wa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu kan ba su dama don ba da gudummawa ga ci gaban zamantakewar tattalin arzikin jihar ta hanyar ayyukan jirgin sama.
Haka kuma Alhaji Dikko Mangal ya nuna godiya recreation da tarbar da aka yi musu a filin jirgin saman wanda Mataimakin Gwamnan Jihar ya jagoranta.
Ya ce kamfanin MaxAirline ya fadada ayyukansa na cikin gida ya hada da Kano, Abuja, Lagos, Maiduguri, Yola da kuma  yanzu Kebbi kamar yadda ta ci gaba da samun ci gaba.
Babban jami’in MaxAirline ya yi farin ciki recreation da batun yarjejeniyar ta MOU inda ya ce suna cikin jihar wata guda da ya gabata don fara-tattaunawar.
A nasa bayanin, Matukin jirgin, kyaftin Usman Saleh ya ce kamfanin MaxAirline ya fahimci cewa jihar Kebbi kyakkyawa ce kuma wurin  yawon bude ido ne, kamar irin  bikin kamun  kifi da al’adun gargaji na  duniya na Argungu wanda ya ci gaba da tara mutane daga sassa daban-daban na duniya.
Kyaftin Usman  dai ya sanar da taron cewa ya kasance kwararren matukin jirgin sama na tsawon shekaru 36,  kuma ba zai yi kasa a gwiwa wurin tashi da saukar sa  a filin jirgin sama na  Sir Ahmadu Bello da ke Birnin-Kebbi a duk lokacin zuwan sa yayi, ya yaba wa Jihar Kebbi da ta amince da  aikin kamfanin MaxAirline.
A cewarsa, kamfanin jirgin saman ya shahara da yin aiki a kan lokaci da kare lafiya, yana mai nuna fatan cewa kawance da alakar da ke tsakaninta da jihar za ta bunkasa.

What's On Your Mind?