Jimillar Jami’an NIS 8,999 Sun Samu Karin Girma Yayin Da Ake Ci Gaba Da Zamanantar Da Hukumar

0
105

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede MFR ya bayar da umurnin lika wa dukkan manyan jami’an hukumar da suka samu karin girma sabbin mukamansu a sassan hukumar daban-daban.

Babandede ya bayar da umurnin ne a ranar Larabar nan 30 ga Satumban 2020 yayin da yake gabatar da jawabi a faretin Kwanturola Janar na wata-wata da aka gabatar ta hanyar hoton bidiyo a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

Jimillar Jami’an NIS 8,999 Sun Samu Karin Girma Yayin Da Ake Ci Gaba Da Zamanantar Da Hukumar

A jawabin nasa ga daukacin jami’an hukumar da ke sassan kasar nan da kuma wadanda suke aiki a ofisoshin jakadancin kasar nan da ke kasashen waje, Babandede ya bayyana musu irin ayyukan ci gaba da ake kan gudanarwa a hukumar wadanda suka hada da mayar da ayyukanta turbar manhajar sadarwa ta zamani, batun karin girma na shekarar 2019, kana da bukatar da ake wa dukkan jami’an su kara shan damara wajen nuna da’a da dukufa ga aiki da kuma tabbatar rikon amana ga kasa da hukumar a cikin ayyukansu na yau da kullum.

Takardar karin girma na shekarar 2019 ga manyan jami’an hukumar wadda aka fitar ranar 28 ga Satumban 2020 ta kunshi sunayen jami’ai 5,351 wadanda suka hada daga masu mukaman manyan mataimakan kwanturola zuwa masu mukaman babban insifekta, kamar yadda Hukumar Gudanarwar Hukumomin Jami’an Tsaron Fararen Hula, Gidajen Gyaran Hali, Kashe Gobara  da kuma Shige da Fice (CDCFIB) ta amince a wata takardar da ta fitar ranar 25 ga Satumban 2020.

Gwamnatin Tarayya Ta Janye Hana Kamfanin Jirgin Emirate Jigila

Idan ba a manta ba, dama Hukumar ta NIS ta lika sabbin mukamai ga wasu manyan Jami’i su 100, da kanana 3,548 da kuma wadanda aka daga darajarsu zuwa manyan mukamai su 118 a ranar 5 ga Agustan 2020. Idan aka hada jimillar wadannan da adadin wadanda aka fitar da karin girmansu ranar 28 ga Satumban 2020, zai zama jimillar yawan jami’an da suka samu karin girma a Hukumar ta Shige da Fice a shekarar 2019 ta kai 8,999.

Sanarwar manema labarai da ta fito daga Jami’in yada labarun NIS, DCI Sunday James ta yi bayanin adadin jami’an da suka samu karin girman dalla-dalla kamar haka: Masu mukaman CIS zuwa ACG su 29, masu mukaman DCI zuwa CI su 71, masu mukaman ACI zuwa DCI su 270, masu mukaman SI zuwa CIS su 529, masu mukaman DSI zuwa SI su 363, masu mukaman ASI zuwa DSI su 78.

Sauran photo voltaic hada da wadanda aka kara wa girma daga mukaman ASI2 zuwa ASI su 32, da masu mukaman CII zuwa CII tech su 403, da masu mukaman DCII zuwa CII su 378, da masu mukaman ACII zuwa DCII su 336. Sai kuma masu mukaman PII da aka kara musu matsayi zuwa ACII su 295, da masu mukaman SII zuwa PII su 1496 da kuma masu mukaman II da aka kara  musu girma zuwa SII su 445.

Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede ya taya dukkan jami’an da suka samu karin girman murna, inda ya kara da cewa manufar karin girman ita ce kara zaburad da jami’ai su yi tsayuwar daka wajen gudanar da aiki kamar yadda aka damka wa hukumar amanar yi.

What's On Your Mind?