Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci Gwamnatin tarayya info kara kason da ta ke rabawa Kananan Hukumomi domin basu damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, jawabin haka ya fito daga bakin Kwamishinan ma’aikatar kananan Hukumomin Jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo lokacin taron wuni biyu domin inganta tsarin gudanar tattara bayanai ga jami’an kananan Hukumomi, da Hukumar tsara rabon kasafin kananan hukumomi ta shirya a Kano ranar Juma’ar info gabata. Kamar yadda Jami’in yada Labaran ma’aikatar Kananna Hukumomin Jihar Kano ya
shaidawa MOBILIZED9JA A YAU Lahadi.
A cewar Kwamishinan, Gwamnatin Tarayya na karbar sama da kaso 52% cikin tsarin, Jihohi kaso 22% ya yinda kananan Hukumomi 774 ke karbar kaso 20.6% wanda ya yi kadan matuka idan akayi la’akari da nauyin dake kan kananan Hukumomin.
Kwamishina Sule Garo ya lura da cewa, karancin aikace aikace ya biyo bayan karancin kason da kannana Hukumomin ke samu daga Gwamnatin tarayya ne, inda ya bayyana cewa akwai bukatar sake duba kason hakan zai taimaka wajen inganta ayyukansu. Garo ya bayyana taron karawa juna sanin da cewa an tsara shi alokacin da ya kamata tare da jadadda cewa taron zai inganta harkokin tattara haraji a matakin kananan Hukumomi, yace Gwamnatin Jihar Kano ta shirya ire iren wadannan tarukan karawa juna sani ga jami’an kananan Hukumomi domin bukatar da ake da ita na inganta harkokin tattara haraji.
Yadda aka halaka wani matashi kan budurwa a Kano
Da yake gabatar da jawabinsa, jagoran tawagar RMAFC wanda kuma shi ne kwamishinan dake wakiltar Jihar Niger, Alhaji Ibrahim Bagudu cewa ya yi, hukumar ta shirya wannan taro ne domin ganawa da juna, tattauna bayanai, fadada tunani da kuma nazarin hanyoyin yadda jihohi da kannan Hukumomi zasu samar da hanyoyin amfani da rumbanan adana bayanai.
Bagudu ya ci gaba da cewa shirin zai taimakawa Gwamnati domin samarwa tare da kiyaye rumbunan adana bayanai wanda zai bayar da dama ga Jihohi domin samar da ingantattun bayanai ga Hukumar RMAFC.
Daganan sai ya bukaci Gwamnatoci dasu kara kokarin sarrafa tattalin arzikinsu domin samun karin kudaden shiga maimakon dogaro da kason Gwamnatin tarayya.
Daga cikin bayanan sakamakon tattaunawar da aka gudanar a karshen taron photo voltaic hada da bukatar daga darajar ofishin lura da albarkartun kasa na mashawarci na musamman domin samun cikakkiyar damar gudanar ayyukansa a ma’aikatar. Haka kuma an shawarci kananan Hukumomi a Jihar Kano da su kara kokari wajen tattara harajin kasa da wuraren haya da sauran kudaden haraji daban daban.
Haka zalika taron ya bukaci sake fasalin tattara bayanai domin tafiya dai dai zamani kamar yadda duniya ke kai, yin amfani da tsarin fasahar zamani na rasitan ajiya, inganta tsarin samar da abubuwan yawon bude ido da amfani da kananan masana’antu da sauransu.
270 total views, 1 views today
Be the first to comment