‘Jaririyar Da Ake Cewa Ta Mutu Bayan Zargin Cire Mata Na’urar Numfashi A Kaduna Na Nan A Raye’

- Advertisement -

‘Jaririyar Da Ake Cewa Ta Mutu Bayan Zargin Cire Mata Na’urar Numfashi A Kaduna Na Nan A Raye’

Daga Abubakar Abba Kaduna

Mahaifiyar jarirya ‘yar kwana shida da haihuwa Malama Fiddausi Anas ta bayyana cewa, diyar na nan da ranta bata mutu ba kuma ta na cikin koshin lafiya.

A tattaunawar da manema labarai suka yi da uwar jariyar Malama Fiddausi Anas a wani asibitin kudi a ake kira Shifa da ke a Unguwar Kanawa cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa ta ce, “Gaskiyar magana diya ta bata mutu ba kuma ta nan a cikin koshin lafiya a Asibitin a Shifa da aka sake kwantar da ita domin a ci gaba da duba lafiyar ta bayan kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki a Kaduna”.

Malama Fiddausi Anas ta ci gaba da cewa, “Malamar jinya mai aiki a ranar a dakin da aka kwantar da mu da ake zargin cewa ta cire wa jaririyar ta na’urar shakar numfashi a ranar da kungiyar kwadago suka shiga yajin aiki ba gaskiya bane, asali ma, taimaka mana ya yi a wannan yanayin”.

A cewar Malama Fiddausi Anas, “Ita malamar jinyar, wacce a ranar ita ce ke kan aiki a dakin da aka kwantar da jaririya ta, karshe ma dai ita ce ta taimaka mana, domin a waccan ranar, jaririya ta ce kusan aka dora a kan na’urar ta numfashi a dakin da aka kwantar da mu”.
Malama Fiddausi Anas wacce mazuniyar garin Rigachikun ce da ke a karamar hukumar Igabi a cikin jihar Kaduna ta kara da cewa, “Babu wani jami’in kiwon lafiya da ke kan aiki a ranar da ya kore mu daga Asibitin saboda yajin aikin na kungiyar kwadago”.

Ta bayyana cewa, “Ita ma malamar jinyar , da kanta take taje ta roki masu kula da Janareta na Asibitin na Barau Dikko cewa, su bar Janaretan ya ci gaba da aiki har zuwa karfe 6 na yammacin ranar saboda akawai jariyar da aka dora a kan na’urar kula da numfashi kuma haka aka yi”.

A cewar Malama Fiddausi Anas, malamar jinyar ta bamu shawarar mu kai jaririya zuwa Asibitin kwararru na 44 da ake Kaduna , amma ba mu je ba domin ba a bamu takardar canjin zuwa wani Asibiti, daga Asibitin Na Barau Dikko ba, sai muka wuce zuwa gida”.

Malama Fiddausi Anas ta kara da cewa, “Daga nan, sai muka je wani Shagon sayar da magani na Abulkareem da ke a Rigachikun, sai ya bamu shawara mu kawo ta Asibitin Shifa da ke a Anguwar Kanawa suka karbe suka sake kwantar da jariyar wacce ko suna ma, ba a riga an yi ba, domin ta na da kwana daya da haihuwa ne, aka kwantar damu a Asibitin na Barau Dikko”.

In za a iya tunawa, an ruwaito Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed el-rufai ya yi zargin cewa, jariryar da aka kwantar a Asibitin na Barau Dikko ta mutu saboda malaman jiniyar da ake aiki a Asibitin na Barau Dikko, solar cire wa jaririyar na’urar shakar numfashi a yayin da Ma’aikatan Asibitin na Barau Dikko ke kokarin amasa kiran kungiyar kwadago ta kasa na tsunduma cikin yajin aiki kan hakkokin wasu Ma’aikatan da gwamnatin jihar ta kora daga aiki.

- Advertisement -