Jam’iyyun Adawa Sun Cancanci Yabo Kan Goyon Bayansu Ga Gwamnatin Neja – Hon. Nuhu

- Advertisement -

Jam’iyyun Adawa Sun Cancanci Yabo Kan Goyon Bayansu Ga Gwamnatin Neja – Hon. Nuhu

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

An yabawa jam’iyyun adawa kan goyon baya da kyakkyawar fahimtar da suke da shi da gwamnatin Neja. Kodineta mai kula da harkokin jam’iyyun siyasa, Hon. Nuhu Ibrahim Ishak ne yayi yabon lokacin da yake zantawa da manema labaru a Minna.

Nuhu Ishak ya cigaba da cewar tun bayan zuwan mulkin Alhaji Abubakar Sani Bello kan karagar mulki bai samu turjiya daga jam’iyyun siyasa ba hakan ya taimaka ga dukkanin zabukan da gwamnatin jiha ta gudanar ya baiwa wasu jam’iyyun adawa samun nasara inda yanzu haka akwai kujerun kansuloli da na karamar hukuma da ba jam’iyyar APC ke rike da su ba.

Duk da matsalolin da gwamnatin ta fuskanta kan matsalar tattalin arzikin kasa da annobar Korona ta janyo, gwamnatin jiha ba tai kasa a guiwa ba wajen kyautatawa ‘yan adawa ba, kamar yadda muka faro tafiyar da gwamnatin nan bisa fahimtar siyasa ina da tabbacin idan muka tafi a hakan a sauran wa’adin da ya rage jihar Neja za ta sama sahun gaba a cigaba.

” Ita kanta hukumar zabe tana yabawa irin yadda tsarin gwamnatin ta ke musamman na hadin kai da kuma tafiyar da zabuka cikin natsuwa da fahimta. Duk da rugumutsin da ake samu a lokacin zabe mu kan ajiye maganar bambancin jam’iyya mu sanya cigaban jihar a gaba, wanda shi ne ya bada sakamako mai kyau ta hanyar jagorancin jihad”.

Ina kiran sauran ‘yan siyasa da su yi koyi da jam’iyyun su wajen baiwa gwamnatin goyon baya dan samun damar cika alkawurran da aka yi lokacin yakin neman zabe, har yanzu ba mu kawo maganar zaben 2023 mai zuwa kamar yadda wasu ‘yan siyasar ke kurari, babban abinda gwamnatin jiha ta sanya a gaba, shi tabbatar kammala ayyukan raya kasa da ya shafi birane da karkaru musamman inganta bangaren noma, ilimi da kiwon lafiya saboda jama’a su anfani tsarin mulkin dimukuradiyya ta yadda tattalin arzikinsu zai bunkasa.

Hon. Nuhu Ibrahim ya yabawa gwamnatin tarayya da ta jiha musamman jami’an tsaro wajen yaki da ‘yan ta’addar da ke kokarin durkusar da jihar, ya jawo hankalin jama’a da su cigaba da yin addu’o’i dan ganin Allah ya kawo mana karshen wannan matsalar a kankanin lokaci. Tabbas raba mutum da muhallinsa abu ne mai zafi, amma gwamna Abubakar Sani Bello bai runtsa ba a kowani lokaci a tsaye yake dan ganin an kawar da ‘yan ta’addar ta yadda kowani dan gudun hijira zai samu damar komawa gidansa, dan cigaba da harkokin yau da kullun.

Ina da tabbacin hanyar da ake bi yanzu ga dukkan alamu akwai nasara sosai, ina yabawa sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki a jihar nan kan kyawawan shawarwarin da suke baiwa gwamnati da jami’an tsaro, dan jama’a su cigaba da yin hakuri da addu’o’i jihar mu za ta samu nasarar ganin bayan rashin tsaro bada jimawa ba.

- Advertisement -