Jami’an yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun ceto wanda aka sace

0
39

Jami’an yan sanda a jihar Zamfara sun dakile harin da yan bindiga suka kai wani gari dake wajen karamar hukumar Shinkafi ta jihar.

A cewar kakakin yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce wannan abu ya auku ne misalin karfe 4:30 na daren Asabar, ChannelTV ta ruwaito.

Jami'an yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun ceto wanda aka sace

SP Shehu ya ce hukumar ta samu labarin cewa yan bindiga sun dira wajen Shinkafi da niyyar garkuwa da mutanen garin.

Majalisar koli ta Shari’ar Musulunci ta jinjinawa gwamna El-Rufa’i

Amma hadakar jami’an PMF/CTU na atisayen “Operation Puff Adder” sun far musu kuma suka kawar da su.

Hakazalika, an ceto wani matashi, Sama’ila Langa, wanda akayi garkuwa da shi a lokacin.

Tuni an mayar da shi wajen iyalansa.

What's On Your Mind?