Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Kasurgumin Dan IPOB

0
86

Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Kasurgumin Dan IPOB

Jami’an tsaron solar kashe wani kasurgumin dan kungiyar IPOB a yau Asabar. Tawagar jami’an ta musamman ta hada da ‘yan sanda da sojoji da kuma na DSS solar kai wani samame ne hedikwatar ‘yan IPOB din da ke kauyen Awomama a Karamar Hukumar Oru ta gabas a jihar Imo da ke kudancin Nigeria.

An ruwaito cewar ‘yan kungiyar IPOB din sune aka dorawa alhakin harin da aka kai hedikwatar ‘yan sanda ta jihar da kuma gidan yari a ranar 5 ga watan Afrilun 2021.

Sun kara kai jerin wasu hare-hare kan jami’an tsaro a kudu maso kudu da kuma kudu maso gabashin kasar nan.

What's On Your Mind?