Hotuna: Jami’an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutane a titin Kaduna-Abuja

0
24

Hukumar mayakan saman Najeriya NAF ta gudanar da atisayen na musamman kan yadda ake ceto mutane a titin Kaduna zuwa Abuja.

An gudanar da atisayen ranar Asabar, 2 ga watan Junairu, 2021 domin horar da jami’an hukumar kan yaki a kasa.

An gudanar da atisayen mai take “Taimako yazo” a titin Kaduna-Abuja.

Wata mai tsohon ciki ta bayyana yadda ta haihu a hannun masu garkuwa da mutane

Kakakin hukumar NAF Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan a shafin hukumar na Tuwita.

A jawabin da yayi, babban hafsan sojin saman, Air Marshal Sadiq Abubakar, yace horar da jami’an hukumar na da muhimmanci domin samun nasara wajen yaki da ta’addanci.

Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutane a titin Kaduna-Abuja

Yace: “Gaba daya manufarmu shine tabbatar da cewa jami’anmu sun kware wajen artabu (da makiya).”

“Hakazalika, atisayen yau wanda aka gudanar kan yadda ake lalube da ceto mutane an yi shi domin inganta kwarewan jami’anmu wajen ceto abokan aikinsu da suka sauka daga cikin jiragensu domin wani aikin gaggawa.”

Kalli hotunan atisayen:

Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutane a titin Kaduna-Abuja

Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutane a titin Kaduna-Abuja

Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutane a titin Kaduna-Abuja

What's On Your Mind?