Jama’ar Garin Gwanki Sun Yaba Wa Jagoran Masarautar Bichi

0
111

Jama’ar Garin Gwanki Sun Yaba Wa Jagoran Masarautar Bichi

Daga Mustapha Ibrahim Kano

Jama’ar Garin Gwanki da ke cikin karamar hukumar bagwai a karkashin masarautar Bichi daya daga cikin masarautu hudu da gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro domin cigaban Kano jama’ar Garin Gwanki solar yabawa Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero kan irin karrama su da mutunta su da Sarkin yayi inda Sarkin ya jagoranci bude wani katafaren masallacin Juma’a da wani bawan Allah Alhaji Bashir Garba danbako Wamban Wapa, dan asalin garin Gwanki ya gina masallaci domin amfanin al’ummar mahaifarsa ta garin Gwanki dake karamar hukumar bagwai cikin Jahar Kano a lokacin da madakin Bichi ya jagoranci jama’ar garin Gwanki zuwa fadar sarkin Bichi domin godiya da ban gajiya kan ziyarar garin Gwanki.

Rahotanni daga garin Gwanki na cewa Mai Martaba Sarkin yaja hankalin al’ummar garin Gwanki akan su kula da wannan masallaci da dan su, abokin su, yayan su, kanin su ya gina kuma cewa masallaci dakin Allah ne dan haka akwai bukatar kula da tsabtace shi da kuma yin ibada na salloli biyar a kowacce rana inda kuma ya umarce su da neman ilimi da yiwa ‘ya’ya tarbiya na sanin Allah da Manzon sa da ahalinsa da sahabbansa da kuma girmama iyaye da sauran magabata domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan gari na Gwanki da ma karamar hukumar bagwai, masarautar Bichi, Kano da ma Najeriya baki daya.

Shi ma Jagoran wannan ziyara a madadin al’ummar yakin mai girma Hakimin bagwai kuma madakin Bichi Alhaji Nura Shehu Ahmad ya mika godiyar sa ga mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero kan wannan ziyara da kuma bude masallacin Alhaji Bashir Garba danbako ya gina inda kuma ya shawarci al’umma da kowa ya bada gudunmawarsa wajen cigaban addini da zamantakewar al’umma a kowanne bangare. Bikin bude masallacin Gwanki ya samu halartar shugaban karamar hukumar bagwai Alhaji Inuwa Zangina dangada da Ustaz Hamza Jibril Gogori da sauran shehunnai da muhimman mutane a yankin da wajen ta.

What's On Your Mind?