Iyan Zazzau Ya Garzaya Kotu Don Kalubalantar Nadin Ahmad Bamalli

0
121

Iyan Zazzau Ya Garzaya Kotu Don Kalubalantar Nadin Ahmad Bamalli

Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu, ya maka gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a kotu saboda nada Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau don maye gurbin Dakta Shehu Idris da ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba.

A cikin takardar karar da ya shigar a babban kotun jihar Kaduna a yau Litinin, Aminu na son kotun ta bada umurnin nada shi Sarki duba da cewa shine ya fi samun kuri’u mafi yawa a zaben da masu zaben Sarki suka yi kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

A ranar 25 ga watan Satumba, masu zaben Sarki na masarautar Zazzau karkashin jagorancin Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu suka mika jerin sunayen yarimomi uku don zaben daya daga cikinsu a matsayin sabon Sarki Zazzau, amma gwamnan jihar Kaduna ya yi kafar ungulu da sunayen. Inda bayan kwanaki aka sanar da Ambasada Ahmad Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

What's On Your Mind?