Inganta Tsaro: Gwamnatin Bauchi Ta Gwangwaje Hukumomin Tsaro Da Sabbin Motocin Sintiri 50

0
120

Inganta Tsaro: Gwamnatin Bauchi Ta Gwangwaje Hukumomin Tsaro Da Sabbin Motocin Sintiri 50

Gwamnatin Jihar Bauchi a karkashin Sanata Bala Muhammad ta rabar da kyautar sabbin motocin aiki guda hamsin (50) kirar ‘JAC Decide-up’ ga hukumomin tsaro domin bunkasawa da inganta aikin tsaron al’umma a fadin jihar.

Motocin sintirin da kudinsu ya zarce naira miliyan 759.5 ne gwamnatin ta sayo don raba wa hukumomin tsaro a kokarinta na dafa wa hukumomin tsaro na gwamnati da ‘yan-sa-kai domin dafa wa azamarsu na tsaro, rabon motocin wanda mai rikon shugaban ‘yan sandan Nijeriya, IGP Usman Alkali Baba ya jagoranci kaddamarwa.

Da ya ke jawabi yayin kaddamar da aikin rabon a gidan gwamnatin Bauchi a jiya, Gwamna Bala Muhammad ya bayyana cewar wannan matakin na daga yunkurin gwamnatinsa na ganin an shawo kan kalubalen tsaro ne da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, rikicin manoma da makiyaya, fada a tsakanin al’ummomi, sara-suka da sauran matsalolin tsaro da suke akwai.

Bala yana mai cewa babu wata al’ummar da za ta samu ingantuwa ko kaiwa zuwa mataki na gaba ba tare da kyautata lamuran tsaronta ba, yana mai daurawa da cewa muddin jama’a suka rungumi dabi’ar zama masu bin doka da oda, ita kuwa gwamnati hakkinta ne ta tabbatar da samar da tsaro da kare musu rayukansu da dukiyarsu a kowani lokaci.

Yaro Da Kudi.. : Kalli Bidiyon Zafaffan Motocin Biyu Da Sarkin Waƙa Nazir Ya Yage a Leda

Ya ce: “Matsalar tsaro hakki ne na mu dukka, don haka jama’a ya dace su bada gudunmawa da hadin kai wa hukumomin tsaro tare da kai musu rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba domin daukan matakan da suka dace a lokacin da suka dace, kawai abu mai sauki shi ne a kai rahoto ga hukumar tsaro mafi kusa domin ganin an yi abun da ya dace kan duk wani motsin da ba a gamsu da shi ba.”

Bala yana mai cewa ta hanyar kai rahoton duk abun da ake fargaba a kansa ne kawai za a taimaka wa hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa na dakilewa da magance matsalar da ke akwai.

Ya ce, duk da cewa Bauchi tana da saukin fuskantar matsalolin tsaro, dole ne gwamnatinsa ta ci gaba da yin duk mai yiyuwa domin wanzar da wannan zaman lafiyar da kwanciyar hankalin jama’an jihar, ya kuma ce, za a kai ga cimma wannan nasarar kyautata tsaro ne da hadin guiwar hukumomin tsaronmu, Sarakunan Gargajiya, limamai, fastoci da dukkanin masu ruwa da tsaki na ganin an inganta da kyautata rayuwar al’umman Jihar Bauchi.

A cewarsa, tabbas motocin suntiri da suka samar wa jami’an tsaron zai taimaka sosai wajen kyautatawa da inganta tsaro ta yadda za su ke samun damar kai dauki ko agaji a duk lokacin da wani abun gaggawa ya taso, ya kuma ce motocin su na da na’urar sadarwa na zamani a cikinsu da sauran kayan aikin da ko a cikin lungu ko karkara ne za su sadar da magana a tsakaninsu.

Shi ma da ya ke jawabinsa na godiya a madadin hukumomin tsaron da suka ci gajiyar motocin aikin, Shugaban ‘yan sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba wanda ya samu wakilci daga mukaddashin shugaban ‘yan sandan Nijeriya AIG, Johnson Babatunde Kokumo, ya bayyana cewar tabbas hukumomin tsaro suna bukatar karin tallafin kayan aiki domin kyautata aikin tsaro a ciki da wajen kasar nan.

IGP Baba ya lura da cewa tabbas ‘yan sanda ma suna da bukatar karin motocin sintiri, don haka ya bayyana cewar da irin wannan tallafin motocin za a samu ingantawa da kyautata tsaro a cikin al’umma.

“Samar da wadannan motocin zai kara kumaji wa jami’anmu na ‘yan sanda wajen ganin solar sauke nauyin da ke kansu na tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’umma. Tallafin ya zo a daidai kan gabar da muke cigaba da kokarin inganta matakan yaki da matsalolin tsaro a kasar nan,” inji shi.

Wakilinmu ya nakalto cewa Rundunar ‘yan sanda solar samu tallafin motoci 16, Sojojin bataliya ta 33 kuma solar amshi kyautar motoci four, jami’an kiyaye hadura FRSC 2, jami’an tsaron farin kaya ta NSCDC kuma solar samu guda 2, sai kuma hukumar kiyaye cinkoson ababen hawa ta jihar Bauchi BAROTA solar samu sabbin motoci four.

Sauran hukumomin da suka samu tallafin solar hada da hukumar tsaron farin kaya ta DSS guda biyu, hukumar HISBA 1, ‘Yan Bijiranti, 1, PSC 1, ‘Yan banga kuma motoci four, jami’an kiyaye cinkoson ababen hawa na ‘yan sanda 1, da sauransu.

What's On Your Mind?