INEC Na Sa Ran Masu Kada Kuri’a Miliyan 120 Su Shiga Zaben 2023

- Advertisement -

INEC Na Sa Ran Masu Kada Kuri’a Miliyan 120 Su Shiga Zaben 2023

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce tana tsammanin akalla masu kada kuri’a miliyan 120 ne za su shiga babban zaben kasar na 2023.

 

Malam Garba Attahiru Madami, Kwamishinan zabe na Jihar Kwara (REC), ya bayyana hakan a Ilorin yayin taron masu ruwa da tsaki kan fadada hanyoyin samun damar masu kada kuri’a a rumfunan zabe a Kwara.

 

Ya kara da cewa, “INEC na shirin yiwa masu kada kuri’a miliyan 120 ne don zaben shekarar 2023 a kasar nan da kuma fadada wuraren tattara kuri’u don fadada wuraren da ake da su yanzu haka wanda ke da matuklkar muhimmanci don rage cunkoson masu jefa kuri’a a yayin zaben, da kuma kawo kusa da rumfunan zaben ga mutane.”

 

Ana gudanar da aikin fadada a sassa da dama na kasar.

 

A cewarsa, Nijeriya ba ta taba yin sama da kashi 35 cikin 100 na masu jefa kuri’a ba yayin zabuka sabanin makwabtanta na Afirka ta Yamma, Ghana wacce ta yi sama da kashi 50 na masu jefa kuri’a a lokacin zabe.

 

Ya ce, “INEC ta yi wa sama da masu kada kuri’a miliyan 84 rajista a babban zaben 2019 tare da rumfunan zabe 119,973 wadanda ba su isa sosai ba amma muna shirin inganta abin a 2023”.

 

Don wannan, hukuma ya lura cewa za ta ci gaba da magance matsalar rumfunan zabe bayan ci gaba da rajistar masu zabe (CBR).

 

Shugaban na INEC ya ci gaba da cewa, da yawa daga cikin wadanda suka cancanci kada kuri’a solar ki jefa kuri’a a ranar zaben saboda nisan rumfunan zabe zuwa gidajensu, wanda hakan ya haifar conkoso.

- Advertisement -