Inda Ranka….Kotun a Kano ta ci tarar gawa Naira 50,000 ko daurin shekara daya

1
44

Kotun majistary mai lamba 44 da ke zamanta a gidan Murtala da ke Kano, ta yankewa wani mutum mai suna Abubakar Bello da tuni da aka ce ya mutu daurin shekara guda a gidan yari.

Mai shari’a Rakiya Lami Saleh ce ta yanke hukunci.

Tun da fari dai an gurfanar da Abubakar Bello a gaban kotun bisa laifin satar mota.

To amma ana tsaka da shari’ar ne aka gabatarwa da kotu takardu na cewar wanda ake tuhuma fa ya mutu.

Hakan ya sa mai shari’a ta rufe shari’ar tunda ba a shari’a da gawa.

To sai dai bayan rufe shari’ar ne kwazam sai aka hango wanda aka ce ya mutun yana yawo gari.

Inda Ranka….Kotun a Kano ta ci tarar gawa Naira 50,000 ko daurin shekara daya

Yadda muka kwato kananan hukumomi 20 daga hannun Boko Haram, Janar Olonisakin

Majiyarmu ta samu wannan labari daga shafin hutudole, hakan ce ta sanya aka yi masa tarko da wata zulakekiyar budurwa, aka kuma sake kamashi.

Dan sandan kotu mai gabatar da kara ASP Ahmad Mukhtar ne ya sake gurfanar da shi gaban kotun bisa zarginsa da laifin satar mota da ake yi masa tun a baya.

Haka kuma mai shari’ar bayan nazari da bincike ta tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi.

Mai shari’a Rakiya Lami Saleh ta yankewa Abubakar Bello daurin shekara guda a gidan yari, ko kuma zabin tarar N50,000.

Sannan kotu ta ce dole ne ya biya N750,000 kudin motar da ya sata tun a baya.

1 COMMENT

What's On Your Mind?