Ina Son Kafa Tarihi A Manchester City, Cewar Sabon Dan Wasa Dias

0
52

Sabon dan wasan bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester Metropolis, Ruben Dias, wanda kungiyar ta saya a cikin wannan satin ya bayyana cewa ya koma kungiyar ne domin ci gaba da kafa tarihi a rayuwarsa kamar yadda ya fara a kungiyarsa ta Benfica a shekarun daya dauka yana buga wasa a kasar ta Portugal.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester Metropolis dai ta kammala daukar mai tsaron bayan, Ruben Dias, mai shekara 23 a duniya daga kungiyar kwallon kafa ta Benfica dake kasar Portugal kan yarjejeniyar shekara shida kan fam miliyan 65.

Ina Son Kafa Tarihi A Manchester City, Cewar Sabon Dan Wasa Dias

Sai dai a cikin cinikin shima dan wasan tawagar Argentina, Nicolas Otamendi, wanda yake buga wasa a kungiyar ta Manchester Metropolis ya koma Benfica kan fam miliyan 13.7 a wani cinikin na da ban kuma shima tuni an kammala.

Dias ya zama dan kwallo na uku da kocin Manchester Metropolis, Pep Guardiola ya dauka a bana, bayan mai tsaron baya Nathan Ake dan kasar Holland daya dauka daga kungiyar Bournemouth  da kuma Ferran Torres dan Sipaniya daga Balencia.

Jimillar Jami’an NIS 8,999 Sun Samu Karin Girma Yayin Da Ake Ci Gaba Da Zamanantar Da Hukumar

Dan kwallon tawagar Portugal, Dias ya fara buga wasa daga karamar kungiyar Benfica daga baya ya koma babbar wacce ya yi wa wasa 113 ya kuma lashe kofin gasar Portugal a kakar wasa ta 2018 zuwa 2019.

Ya kuma buga wa tawagar Portugal wasa 19, ana kuma sa ran zai dinke barakar bayan Manchester Metropolis wacce a wasan daya gabata kungiyar kwallon kafa ta Leicester Metropolis ta zura mata kwallo biyar a gasar Premier League a karshen mako.

Sai dai bayan an gabatar dashi a gaban manema labarai dan wasan ya bayyana farin cikinsa da kasancewa a daya daga cikin manyan kungiyoyin duniya sannan a hannun daya daga cikin manyan masu koyarwa na duniya wato Pep Guardiola.

“Manchester Metropolis babbar kungiya ce wadda a duniya yanzu tana daya daga cikin manyan kungiyoyi saboda haka samun damar buga wasa a wannan kungiya ba karamin aiki bane kuma ina fatan zan kafa tarihi” in ji Dias

Sayan da Manchester Metropolis ta yiwa dan wasa Dias shine ya kawo adadin kudi fam miliyan 400 da kociyan kungiyar Pep Guardiola da ya kashe a wajen sayan ‘yan wasan baya idan aka hada da ragowar ‘yan wasan baya da kungiyar ta saya a baya a lokacin na Guardiola.

What's On Your Mind?