Ina son aure yaro matashi dan shekara 25 zuwa 30~ Inji shugabar kungiyar muryar Zawarawa ta Kano

- Advertisement -

Hajiya Altine Abdullahi ta bayyana cewa, tana matukar son auren yaro matashi sabon jini dan shekara 25 zuwa 30.kamar yadda jaridar mikiya na ruwaito.

Matar ta bayyana cewa, akwai fa’ida mai yawa tsohuwa ta samu karamin yaro ta aura.

Akan haka matar ta bayyana cewa a shirye take data auri matashi dan shekara 25 zuwa 30 matukar ta yi shawara da ya’yan ta.

Dudda yake matar ta bayyana cewa koda ace ya’yanta basu amince ba ita a shirye take data auri matashi mai kananan shekaru, tun da har bai sabawa addinin musulunci.

Matar ta ci gaba da cewa” Da ace an kama macce da karamin yaro tana lalata ai gara ace auren sa ta yi”.

Shin ya kuke kallon kalaman wannan mata ne?

- Advertisement -