Ina Matukar Farin Ciki A PSG -Neymar

0
88

Ina Matukar Farin Ciki A PSG -Neymar

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar Jnr, ya ce wannan kakar ta bana ita ce yake cike da farin ciki a kungiyar, duk da rade-radin da ake kan makomarsa a Faransa.

Har yanzu Neymar, dan kasar Brazil, mai shekara 29 a duniya, bai saka hannu ba a kan tsawaita zamansa a kungiyar ta PSG, bayan da yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar wasa ta badi.

An ta alakanta shi da cewar zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona wadda ya bari ya koma PSG kan fam miliyan 200 a shekarar 2017 a matakin mafi tsada a duniya kuma har yanzu babu dan wasan da ya fishi tsada a duniya.

Neymar ya ce ”Wannan kakar ta bana PSG ta kara bunkasa, kuma muna sa kwazo domin kara daga darajar kungiyar saboda haka muna matukar son lashe kofin zakarun turai na Champions League.”

A jiya ne Laraba Paris St Germain ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Manchester Metropolis a wasan farko na dab da karshe a Champions League wasan da ya kasance zakaraan gwajin dafi ga sabon kociyan kungiyar, Mauricio Pochettino.

Neymar ya ci kwallo shida a karawa bakwai a Champions League a bana, wanda ya zura kwallo 14 jumulla a wasanni 24 a dukkan fafatawa sannan PSG wadda ta nada Mauricio Pochettino kocinta a cikin watan Janairu tana ta biyu a kan teburin Ligue 1 da tazarar maki daya tsakaninta da Lille.

What's On Your Mind?