Ina Mamakin masu Cewa Abduljabbar yana Zagin Sahabbai?

0
36

Ya kamata fa kowa ya sani, Nigeria ƙasa ce da ba ruwanta da Addini, don haka dokar ƙasa ta ba da kowa damar ya yi Addininsa yadda yake so, bisa yadda ya fahimta. Don haka kar kowa ya tsangwami Aduljabbar a kan ra’ayoyinsa da yake bayyana su a kullum, ko da solar cika da zagin Sahabbai, da ƙaryata Sunna hujjar Muslunci, da zagin magabata da sauran manyan Malaman Addinin Muslunci.

Ai shi Abduljabbar gaskiya yake faɗa, daga littatafan Hadisi yake cirowa. Kuma waɗanda ake cewa su ne Malamai in solar isa su musa.

Ina Mamakin masu Cewa Abduljabbar yana Zagin Sahabbai?

Allahu Akbar! Shahararren Dan Kwallon Kwando Na Duniya Stephen Jackson Ya Karbi Musulunci

Wannar ita ce hujjar Abduljabbar da yaransa, a kan abin da yake yi na zagin Sahabbai, da koya wa matasa keta alfarmar Hujjojin Addinin Muslunci, da cin zarafin manyan mutane a cikin al’ummar Musulmi, tun daga kan abokan Annabi (noticed) da sarakanansa kuma khalifofinsa, da matansa da ƴaƴansa da masu yi masa hidima da sauran almajiransa har zuwa kan Tabi’ai, mabiyansu, zuwa kan na bayansu Limaman Addini, har zuwa kan Malaman Muslunci na kowane ƙarni har zuwa wannan zamani.

To mutane da yawa in solar tashi a kan wannan kawai suke tsayawa, alhali lamarin Abduljabbar ya girmama, ya faɗaɗa, ya tumbatsa har ya wuce wannan, ya isa kan jagoran al’ummar gaba ɗaya. Kai, shugaban ƴan-adam gaba ɗaya, wato Annabi Muhammadu Manzon Allah (noticed).

Mutumin da yake danganta munanan maganganu da ƙazaman aiyukan assha ga Annabi (noticed), yake keta mutuncinsa, yake yaga alfarmarsa, yake zubar da ƙimarsa, yake danganta masa Fyaɗe da makamantansa!

What's On Your Mind?