Ina Bai Wa Gwamnati Shawara Kan Tsaro Amma… In Ji IBB

- Advertisement -

Ina Bai Wa Gwamnati Shawara Kan Tsaro Amma… In Ji IBB

Daga Mahdi M. Muhammad,

Tsohon Shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana cewa, ya kasance yana baiwa gwamnati shawara kan yadda ya kamata a magance kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta amma ba ya yin surutu sport da hakan.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa ranar Lahadi.

Ya ci gaba da cewa, ya zama dole ga ‘yan kasa da gwamnati su hada kai da aiki tare don cimma sakamako.

Akan ko ‘yan siyasarmu suna taka rawar da ake so wajen kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar, ya ce, akwai abubuwa da yawa da suka kamata su daidaita.

“Idan suka yarda su zauna su yi tunani, na yi imanin za a cimma nasara,” in ji shi.

Lokacin da aka kara tambayarsa kan irin wadannan abubuwa don a daidaita su, ya ce, yana da muhimmanci a tara sojoji da sauran hukumomin tsaro tare, a tallafa musu kuma a sanar da su cewa ‘yan kasa suna bayansu.

“Ku samar masu da duk abin da suke bukata kuma ku sanar da su cewa wannan ita ce kasarsu, ba su da wata da ya fi wannan,” in ji shi.

Da aka tambaye shi ko ya yi imani sojojin Nijeriya suna bukatar makamai na zamani, sai ya ce, eh, suna bukata.

Ya kara da cewa, “su kuma suna bukatar a basu horo kan yadda za su yi amfani da makaman na zamani, ba don samun makamai ba kawai su mika su garesu. Ya kamata a basu horo.”

A kan ko ya taba bai wa Gwamnatin Tarayya shawara kan hanyoyin da za a kawo karshen rashin tsaro, wanda a yanzu ya kutsa cikin jiharsa ta asali (Neja), sai ya ce, “muna ba da shawara, kamar yadda zamu iya, amma ba mu yin surutu sport da hakan. Ba mu sanar da cewa wannan shi ne abin da muke fada ba.”

“Ya kamata mu hada kai, ya kamata mu tallafawa wadanda ke kan mulki, dukkanmu muna aiki don cimma buri daya. Tsakanin shugabanni da ‘yan kasa muna bukatar zaman lafiya da hadin kai da jituwa,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan matsalar rashin tsaro, kowace gwamnati tana da gogewarta akai, amma idan muka hada kai zamu iya magance matsalar. Na tuna yadda muka kwashe shekaru three muna yakin basasa, mutane solar goyi bayan gwamnati, gwamnati tayi iya kokarin ta, ta sayi abinda ya kamata, wadanda suka yi yakin solar kasance an fahimci cewa wannan kasar ce mafi kyau a gare su.”

“Ba wai kawai a Nijeriya ba, kasashe da dama solar gamu da irin wannan matsalar, wasu na fama da ita tsawon shekaru goma, amma ta hanyar kokarin hada kai solar fita daga ciki. Na yi imani za mu iya fita daga wannan matsalar,” in ji shi.

“Duk ‘yan kasa da wadanda ke mulki suna kokari, amma ya kamata mu san cewa ba abu ne mai sauki ba,” in ji shi.

- Advertisement -