IN KA KI JI: Gajeren Labari

- Advertisement -

IN KA KI JI: Gajeren Labari

Daga Hauwa’u Adam Suleiman (Jidda Washa)

Cikina ne ya kama wani irin kyarma tamkar ana kada masa gangi, cikin motar gaba daya kowa ya tsure daga masu ihu sai masu salati, lokaci guda muka kama kyarma tamkar ana shadi.

Harbin bindigar ke kara tsananta, yayin da direbanmu ke gudun fanfalaki tamkar ba gobe, duk gaba daya na kidime ba abin da ke fita daga zuciyata sai salati da tunanin bijirewa maganar Inna da na yi na taho ba tare da izininta ba. Can kamar daukewar wutan lantarki, bayan kiftawa da Bismillah lokaci guda harbin ya tsaya cak, inda kowanne mahalukaton na cikin motar ya dunga sauke ajiyar zuciya ba kaukautawa tamkar an kammala gasar gumurzun kiba na tsere.

 

Mun samu tafiyar mintina akalla ba akasara ba don zai iya kaiwa dakika arba’in ko fiye da hakan, hankalin kowa ya dawo gare jikinsa, wasu daga cikin motar har solar fara hirar siyasa da ta boko haram. Daidai wani daji, da zai sada da mu ya zuwa garin da zamu, wato jihar Kodau. Kamar a mafarki, muka ji hargagin wani sautin harbi na bindiga, wanda tunda nake ban taba jin irin karar bindigar ba. Ras kirjina ya buga.

“Wayyo Allah kudina!”

Cewar wani matashin saurayi fari mai saurin magana ya fada gami da dora hannaye biyu a tsakiyar kai.

 

Dirar wasu manyan kartai muka ji daga cikin wata mota mai matukar kyau da daukar hankali, duk ilahirin fuskokinsu a rufe, suna ta magana da junansu amma ko kadan Hausar su bata fita irin tamu, wadanda suka hadar da mata manya masu sanfurin samudawa guda biyu dauke suke da bakaken kaya ba dankwali a kayuwansu, gashin kansu bakin kirin amma babu halamun gyara balle kitso, ragowan biyar din maza ne tika tika tamkar bugun adawa su ma shigarsu iri daya.

 

Cikin wani razanannen ihu na tsawa, ɗaya daga cikinsu ya ce “Kowa na cikin motar nan ya sauko ya rusuna a ƙasa”

 

Wani kara mara misaltuwa cikina ya sake bugawa, inda hantar cikina ta kada, wani tsillin gudawa ne ya so ya kufce min, kowa da ganinsa duk mun tsure, sai raba idanu muke tamkar wadanda aka ritsa a gidan ‘yan sanda.

Jiki na karkarwa haka muka sauka daya bayan daya cikin azama, da yawa daga cikinmu wasu solar bata jikinsu da fitsari, gudawa da kuma kuka.

 

“Duk wani dan shegiya daga cikinku da ya sake min kuka ko fitsari ko kashi babu makawa sai ya cinye sa ko ya lashe kayansa tas”

 

Ras, kirjina ya sake tafiya garin bugu cike da rashin lissafi. Wani rubabben kango suka kai mu, suka zube mu kasa tamkar kayan wanki, inda suka yi mana kawanya, sannan suka bi kowannen mu da bulala goma goma.

“Ina son kowa ya mikawa Shaidan wayarsa domin za a kira iyayenku a fada musu kudin fansarku”

A karo na uku kirjina ya sake wani ganga, da sauri na dago da kaina sama, cikin zaro idanuna waje, nanne na kasa daurewa damuwata har wasu tsirarin hawaye suka kufce mini. “kai dalla ba mu wayarka, wawa kawai, shashasha” Wata murya mai ban tsoro ta fada gami da zuba min yatsu a fuska, sanadin da ya sada ni da kasa har na kai ga rasa fahimtata na tsurarin dakiku.

 

Bayan faduwar yammaci, magariba ta bugo sallama, dukkanin mu ba mu san halin da muke ciki ba, ni dai tunanina dai bai wuce a kan abu biyu ba, na farko mu talakawa ne wanda na abinci wani zubin gagarar mu yake yi, sai kuma kin jin maganar Innata da na yi na bijirewa umarninta saboda son zuciyata, wanan shi ake kira da tashin hankali wanda ba a sa ma sa rana ko lokaci, lallai yau ita ce ranar tonan silili gare ni na duniya.

 

“kai! kai!kai!”

Wani mai runannun idanu jazur tamkar gauta ya fada cikin zare idanu yana nuna ni da wani sankamemen manuninsa.

“Lallai za mu kashe ka idan har ba mu ji bayani daga wurin Uwarka ba” Kalamansa ne suka dunga yi min shawagi a tsakiyar kwakwalwar kundin kaina. Za mu kashe ka! na tambayi kaina cike da kyarmar maganar, nan da nan na ji wani irin hawaye gaiyar sodi solar min hawan kawara wanda ba sa jin hakuri tare da wasu majina marasa kiranye suka dunga sharbo min.

Abin mamaki kusan dukkanin ilahirin wanda ke gurin kuka ne ya zamar masa sana’a ba kaukautawa.

 

Yau kimanin mako daya kenan muna cikin halin ha’ula’i a cikin wannan bakin kangon, kullum tunanina daya a wani irin hali Inna take ciki, ina da ina za ta karade wajen neman kudin fansata? na sake tambayar kaina a karo na biyu, ga shi kullum sai an yi mana bulala goma goma, abinci ma sau daya suke ba mu a yini, ko ta sallah ma ba a yi duk da hakan ya tsaya min a kokon ramin zuciyata.

 

 

“Da kai da kai da ke, ku taso mu tafi yau Allah ya kwace ku”

“Alhamdu Lillah!”

Suka furta inda suka mike da sauri suka bi sahun sa. Abu dai dada gaba gaba yake, kowa an biya kudin karbar fansarsa saura mu biyu, ni da wani saurayi bakin kirin tamkar makuba, yau ga shi saura kwanaki uku daga cikin kwanakin da aka sanyo na jarabawar mu ta unibasitin da nake yi a garin da na bari na shigo cikin wannan ibtila’in a Jihar KOWA.

 

Tagwayen makonni solar shude daga cikin wata daya da muka share a wannan bakin kangon, babu wani labari na abin sha’awa dangane da batun tsirana daga hannayen azzaluman nan, duk na rame na fita a haiyacina saboda irin azabar da suke ba mu ni da matashin saurayin nan, kullum sai solar yi mana bulala goma goma secure zuwa dare sannan su samu wanki da kuma yi musu tausa gami da daga bulo zuwa safa da marwa.

Yau take ranar da ba zan taba mantawa ba a rayuwata ba, saboda tsabar zulumi na rasa da wani suna zan radawa ranar domin na ga aya ta rayuwar duniya.

Zaune muke a rakabe a jikin wani bango na cikin kangon, sai ga wani mahalukaton ya shigo cikin zafin nama, inda ya yo kanmu da faɗin.

 

“Yau zaku daina jin kamshin duniya sai dai na barzahu” Maganar da ta haddasa min wani faduwar gaba mai tafiya da hanjin ciki da ruwan sassan dake cikin jikina da gangar waje suka kama kyarma da kidima. Wani irin tsorata na yi, Matashin nan take ya kwalla wani razanan nan ihu, wanda tsigar jikina sai da ta tashi, lamarin da ya haddasa min tausayinsa, inda Kasurgumin basamudan nan kato ya sharara masa wani gigitaccen mari, lamarin da ya sa Matashin ya zube a kasa sumamme, haka ya dunga jan sa a kasa cikin birjin ciyayi da duwatsu da gwazazzabai har muka isa bayan wani daji gab da wani kwari mai dauke da siradin nisa na rami.

 

“Aikin ka ya yi kyau, Boka”

Inda suka sa dariya, cikin wani mummunan sauti mara daɗin fasaltuwa. “Muguwa! ke ce zaki karasa wancan na kusan”

 

Inda ya kai hannu ya nuna wannan Matashin da ke kwance rai a hannun Allah, da sauri ta karaso tare da saita kan bindigarta ya zuwa kan kirjinsa, kan ka ce kwabo ta zuba masa dalmar alburushi, wanda ya yi sanadiyar fitar wasu danyun jini daga kirjin. Kafin su furta wata kalma, tuni na saduda na bar wa Allah komai, ban da istigifari ba abin da nake yi, saboda na san ba za su bar ni ba.

 

“Dawo nan ka tsugunna sannan ka juya ka kalli bayanka” Wata murya mara imani da tausayi ta fada, da hanzari na bi umarnin sa. “Makira taho ga aikinki ya fito, zo ki aika mana shi kiyama, su je ma taho, tunda iyayensu ba sa son su”

 

Da sauri na runtsa idanuna, sannan na fara maimaita kalmar shahada cikin wani kufceccen hawaye wanda ya taho ba da umarnina ba. Cikin kiftawa da Bismillah, na ji dirar wata kara da kugi, wanda ban san ta me ye ba, sakamakon idanuna a rufe ne.

 

“ku mu gudu! ga su nan solar karaso za su kashe mu” Abin da na ji daya daga cikinsu ya furta, da sauri na bude idanuna, wani katon wadataccen jirgine da ake kira ds jirgi mai sauƙar ungulu ya nufo ni, wanda tuni su solar bar wurin a dari, da sauri na fara neman tashi don ceton raina amma na ji wani sauti na faɗin. “kar ka motsa idan ba haka ba, zan sauke maka dalma”

 

Jin haka ya sa na dakata da kudurina na ki mikewa dan ganin kayan sojojin dake jikinsu. Bayan mun dawo jihar Kowa, kai tsaye ma’ajiyar sojoji muka nufa inda suka dunga min tambayoyi a yadda na tsinci kaina a wannan halin, inda na kwashe labarin komai na fada musu.

 

“Innata! Innata!” Abin da na tsinci bakina na furtawa, inda na ga an kallo ni, bisa halamu maganar zuciyata ta fito sarari. “Innarka tana tafe domin mun sanar da labarin cikiyarka a gidajen tibi da gidajen rediyo” Wani nauyayyen ajiyar zuciya na sauke wanda ya tarar min tun gabanin makonni uku da suka gudana. Bayan mintina goma da kammala cin abincina na jiyo sautin Inna cikin kuka ta na fadin. “Yana ina Faisal? yana ina Faisal?” Haka ta runka fadi har ta karaso inda nake a tsugunne ta taho ta rungume ni tare da shafa min kai da faɗin. “Ba ga irinta ba Faisal! lokacin da na ce maka karka je wannan garin saboda abubuwa da suke faruwa, amma ka tubure sam ka kekasa kasa ka furzar da maganata ka yi gaban kanka, to yanzu dubi halin da ka shiga, da yanzu labarin ya sauya daga rayuwa zuwa mutuwa”

 

Shiru na yi saboda tausayin Innata ni kadai ta haifa ga shi ta tsufa, wasu hawaye ne suka sake kufce min, inda Inna ta dora da. “wannan kaddara ce babba, an sauke karatun alkur’ani sau ba adadi duk akan ka, sanadinka na je kauye na sayar da abin da mahaifinka ya mallaka da dabbobinsa, amma san ko rabin kudin da suka nema daga miliyan uku ɗin ba a samu ba, ko da na saka gidanmu a kasuwa yau ne ranar da za a kawo min kudin, sai ga shi Allah ya kwato ka da kyar, lallai na sha wahala Faisal a dan takin nan, saboda haka wannan darasi ne gare ka ga kuma waninka”

- Advertisement -