IGP Adamu ya haramta wa jami’an SARS wasu jerin ayyuka

0
56

Sifeta janar na ‘yan sanda, M.A Adamu ya dakatar da ma’aikatan FSARS daga cigaba da ayyukansu, sakamakon korafin da ‘yan Najeriya suke yi akan ‘yan sanda na ta’addanci.

Ba su kadai wannan umarnin ya shafa ba, har da ma’aikatan STS, IRT da kuma ACS.

An dakatar da ma’aikatan daga yin ayyuka kamar sintiri, tsayawa bincike, ba da hannu da sauran ayyukan da suke yi a kan tituna.

IGP Adamu ya haramta wa jami'an SARS wasu jerin ayyuka

Sakamakon rashin sanin makaman aiki irin na su kamar yadda a kan samu lauyoyi, ‘yan kasuwa, fastoci da sauran su suke yi.

Sannan shugaban ‘yan sandan ya dakatar da duk wani dan sanda da yin sintiri ko kuma wasu ayyukan ‘yan sanda da kayan gida. Dole ne su dinga saka kayan aiki.

Na kama matata ta na cin amanata da wani magidanci – Tsohon minista FFK

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.

Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.

Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga ‘yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai. Shugaban kasar ya kara da amincewa da cewa, kasar na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban a sassan kasar.

What's On Your Mind?