Idan Har Ana Son Tsaro A Makarantu: A Tarwatsa Dazukan ‘Yan Bindiga Da Bama-bamai –el-Rufai

0
260

Idan Har Ana Son Tsaro A Makarantu: A Tarwatsa Dazukan ‘Yan Bindiga Da Bama-bamai –el-Rufai

Hanya guda daya da za a iya samar da tsaro a makarantu ita ce a kawar da dukkan ‘yan bindiga daga doron kasa a Nijeriya tare da kaddamar da farmakin tarwatsa dazukan da suke ciki da bamabamai.

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fadi hakan a ranar Talata a Abuja a wajen wani taro kan samar da tsaro a Makarantun Nijeriya.

A cewarsa, ya kamata Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta afka wa dazukan da ‘yan bindiga ke buya da bamabamai.

Ya ce, “Babu wanda ke zaune a cikin dajin da ba shi da laifi, hakan ya sa dole ne mu kashe su duka.

“Babban hafsan sojin saman yana yin matukar kokari don hakan ya haifar da raguwar ayyukan ‘yan bindiga a cikin ‘yan kwanakin nan,” in ji Gwamnan.

Gwamnan ya kuma ba da shawarar cewa, ya kamata a sayo jirage marasa matuka a tura su don taimaka wa a yaki da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata muggan laifuka.

Ya kara da cewa, za a iya dakatar da ‘yan ta’adda idan mutane suka daina tattaunawa da su tare da biyansu kudin fansa.

“Mutane suna tambaya ko an sace yarona kuma na ce ba zan biya ba, shawara ce ta kashin kai, wanda ba dukkanmu muke goyon baya ba. Don haka hanya daya tilo ta dakatar da ‘yan ta’adda ita ce ta kashe su duka,” in ji shi.

Yan Sanda Sun cafke Wasu ‘Yan Damfara Uku Da ‘Yan Bindiga Biyu a Katsina

Dangane da batun biyan wasu mutane don su daina ta’addanci da ake ganin gwamnatin el-Rufai ta yi hakan a baya, gwamnan ya yarda cewa gwamnatinsa ta bi sawun wasu Fulani masu zafin rai kuma ta biya su kudi don su daina kashe ‘yan kudancin Kaduna da sauran mazauna yankin, amma ga dalili, “Kudancin Kaduna, ba mu fahimci abin da ke faruwa ba da farko, kuma mun yanke shawarar kafa kwamiti a karkashin Janar Martin Luther Agwai, don gano abin da ke faruwa a can. An kafa kwamitin ne don dakatar da asalin matsalar da ta faro tun daga rikice-rikicen bayan zaben shekarar 2011.”

Ya ci gaba da cewa, “Fulani makiyaya daga ko ina cikin Afirka suna kawo shanunsu zuwa Kudancin Nijeriya. Lokacin da ruwan sama ya fara a kusan watan Maris da Afrilu, sai su fara tafiya da su don komawa ga al’ummominsu da kasashensu. Abun takaici shi ne, lokacin da suke tafiya da shanunsu a fadin Kudancin Kaduna ne aka gudanar da zabukan 2011 kuma rikicin ya ritsa da wasu daga cikinsu. Wasu daga cikinsu photo voltaic fito daga Nijer, Kamaru, Chadi, Mali da Senegal. Fulanin suna cikin kasashen Afirka 14 kuma suna keta kasar nan da shanu. Da yawa daga cikin wadannan mutane an kashe su, an sace shanun, wanda hakan ya sa suka shirya kansu kuma suka dawo ramuwar gayya.

“Don haka yawancin abubuwan da ke faruwa a Kudancin Kaduna a zahiri photo voltaic fito ne daga wajen Nijeriya. Mun gano cewa Marigayi Gwamna Patrick Yakowa ya sami wannan bayanin kuma ya tura wani ya zagaya wasu daga cikin wadannan al’ummomin Fulani, amma tabbas bayan ya mutu, duk abin ya tsaya. Abinda muka gada kenan. Amma kwamitin Agwai ya kafa hakan. Mun dauki wasu matakai. Mun samu wasu gungun mutane da ke ta zagayawa suna kokarin binciko wasu daga cikin wadannan mutanen a Kamaru, Jamhuriyar Nijer da sauransu don fada musu cewa akwai wani sabon gwamna wanda bafulatani kamarsu kuma ba shi da matsala wajen biyan diyyar rayukan da aka rasa kuma yana rokonsu da su daina kisan,” in ji shi.

Ya ce, “A mafi yawan al’ummomin, bayan su ji wannan wannan rokon photo voltaic ce photo voltaic yafe. Akwai guda daya ko biyu wadanda suka nemi diyyar kudi. Photo voltaic ce photo voltaic yafe mutuwar mutane, amma suna son a biya su diyyar shanunsu. Mun ce babu matsala, kuma mun biya wasu. Kamar yadda ya gabata kamar makonni biyu da suka gabata, kungiyar ta je Jamhuriyar Nijer domin halartar wani taron Fulani da suke gudanarwa a kowace shekara tare da sako daga wurina.”

What's On Your Mind?