Ibrahimovic Ya Sake Sabon Kwantiragi AC Milan

0
61

Ibrahimovic Ya Sake Sabon Kwantiragi AC Milan

Dan wasa Zlatan Ibrahimovic ya sake saka hannu a kan yarjejeniyar ci gaba da buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta AC Milan zuwa kakar wasa daya bayan doguwar tattaunawa da akayi tsakanin dan wasan da shugabannin kungiyar.

AC Milan ta ce Ibrahimovic ya amince zai ci gaba da wasa a Italiya, bayan wasanni 130 da ya yi wa kungiyar da cin kwallo 84 sannan dan dan wasan tawagar Sweden shi ne kan gaba a ci wa kungiyar kwallo a bana mai 17 a raga a wasa 25 da ya yi a dukkan fafatawa.

Ibrahimovic wanda ya cika shekara 40 a cikin watan Oktoba ya koma kungiyar AC Milan a karo na biyu a watan Janairun shekara ta 2020, bayan da ya bar LA Galady mai buga gasar Amurka ta Major League.

dan wasan ya ci kwallo 28 a karawa 45 tun komawarsa Italiya da buga wasa kuma kwazon da Ibrahimovic ke yi a AC Milan ya sa tana ta biyu a kan teburin gasar Serie A da tazarar maki 10 tsakaninta da abokiyar hamayyarta, Inter Milan ta daya a teburin gasar bana.

Kawo yanzu saura wasanni shida-shida a karkare kakar bana ta Serie A ta Italiya kuma tuni alamu suka nuna cewa kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ce zata lashe gasar ta bana sakamakon rashin kokarin kungiyar Juventus, mai kare kambu.

What's On Your Mind?