Hukuncin wanda maziyyi ko maniyyi ya fito masa alhali ya na azumi daga bakin Aminu Daurawa

0
516

Hukuncin wanda maziyyi ko maniyyi ya fito masa alhali ya na azumi daga bakin Aminu Daurawa

Wani Bawan Allah ya aiko wa Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa tambaya, inda ya nemi fatawa a kan zubar da maniyyi a lokacin da mutum yake azumi.

Wannan mutum ya bayyana cewa ya na cikin yin waya da budurwarsa a wayar salula, sai ya ji maniyyi ya fito daga gabansa, alhali azumi ya na bakinsa.

Kafin ya amsa tambayar, babban malamin na musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ja-kunne a kan yin waya irin wannan a lokacin da ake azumi.

Shehin malamin ya ce ganganci ne mutum ya na dauke da azumi, kuma ya rika yin wayar da za ta iya motsa masa sha’awa a cikin watan azumi na Ramadan.

Aminu Ibrahim Daurawa ya nakalto fatawar babban malamin fikihu nan, Ibn Abi Zayd Al-Qayrawani, wanda ya ce irin azumin wannan Bawan Allah ya karye.

Sheikh Al-Qayrawani a littafinsa na Risala, ya ce wanda ya zubar da maziyyi da gangan a sanadiyyar sha’awa zai kama baki, sai ya rama azumi daya daga baya.

Daga Karshe Daurawa Yayi Magana Akan Hukuncin P.O.S Fahimta Ta Akan Sana’ar P.O.S !!

Haka zalika a fatawar bajimin malamin, duk wanda ya kai har ga zubar da maniyyi a lokacin azumi, sai ya yi kaffara; zai yi azumi 61 bayan watan na Ramadan.

Wani Bawan Allah ne ya wallafa bidiyon wannan amsar tambaya a shafinsa na Twitter. Da alamu an yi karatun ne a garin Gombe inda malamin ya saba yin tafsiri.

A kwanan baya an yi wa wani malami irin wannan tambaya, inda ya ba mai neman wannan amsa shawarar ya fara da yin aure domin ya magance sha’awarsa.

A wani kaulin da ya sha ban-bam da fatawar malaman mazhabar malikiyya, fitar maziyyi ba ya karya azumi, amma an hadu a kan hakan zai nakasa ladar mutum.

A cikin irin wannan shirye-shirye na mu na goron Ramadan, kwanakin baya mun kawo maki jerin abubuwa 10 da ya kamata kowane Musulmi ya kiyaye da Azumi

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana sport da abubuwan da ake bukatar mai azumi ya kiyaye. Daga ciki akwai karatun Kur’ani da kuma yawan yin salloli.

Supply: Legit.ng

What's On Your Mind?