Hukumomin Saudiyya Sun Ce Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba

- Advertisement -

Hukumomin Saudiyya Sun Ce Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba

Rahotanni daga hukumomin Saudiyya solar tabbatar da ba a ga watan Shawwal ba, wanda hakan ke nufin za a tashi da azumin na 30 a gobe Laraba. Sallah sai ranar Alhamis kenan. Kamar yadda rahoton kwamitin ganin wata na kasar ya ayyana.

An sa ran za a iya ganin watan a yau Talata 29 ga watan Ramadan, amma bayan duba watan da hukumomi masu alhakin duba watan suka yi solar bayyana cewa lallai da matukar wahala a iya ganin jinjirin watan a yammacin yau Talata, don haka za a cika azumin 30, sai ayi idin karamar Sallah a ranar Alhamis.

- Advertisement -