Hukumar Zakka Ta Kano Ta Raba Naira Miliyon 10 Ga Mabukata

0
113

Hukumar Zakka Ta Kano Ta Raba Naira Miliyon 10 Ga Mabukata

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Hukumar Zakkah Da Khubusi ta Jihar Kano, karkashin kulawar Shugaban Hukumar da babban Darakta, Safiyanu Ibrahim Gwagwarwa da sauran shugabanninta suka jagoranci bikin rabawa talakawa mutum dubu daya Zakkar Naira miliyon goma. Alokacin bikin kaddamar da wannan abin alhairi, kowane Mutum guda daga cikin Mutum dubu daya da aka ambata ya amfana da Naira dubu Goma.

Da yake gabatar da jawabinsa alokacin taro, Gwamnan Jihar Kano Wanda babban Kwamandan Hukumar Hisba na Jihar Kano  Sheikh Muhammad Ibn. Sina ya wakilta, ya tunawa al’umma alfanun dake cikin fidda hakkin Allah, sannan kuma ya tunatar da ‘yan Majalisun dokokin Jihar Kano, ‘yan Majalisar wakilai da Sanatocin Jihar Kano guda uku, inda ya tunatar dasu takardun da Hukumar Zakka da Khubusi ta Jihar Kano ta gabatar masu domin bayar da tasu gudunmawar.

Da yake gabatar da jawabinsa alokacin taron, babban Daraktan Hukumar Zakka da Khubusi Na Jihar Kano Alhaji Safiyanu Ibrahim Gwagwarwa ya bayyana aniyar Hukumar na tabbatar da ganin masu hannu da shuni na bada zakkarsu ga wannan Hukuma.

Yace zuwa yanzu akwai tsare tsare masu yawa da muka gabatarwa Gwamnatin Jihar Kano Kuma muke neman sahalewar Gwamnati, domin Samar da dokar da zata tabbatar da cewa bba Wanda zaiyi wata takara ko samun nadi Kan wani mukami a Jihar Kano har sai ya nuna shaidar biyan zakkar sa. Hakan zai taimaka kwarai wajen tsarkake dukiya tare da taimakawa mabukata a Jihar Kano.
Daga cikin wadanda suka bada Zakkar da aka rabawa mabukata a wannan Rana, akwai Alhaji Aminu Dantata wanda ya bada Miliyon biyar, sai kuma ragowar mutune biyu inda daya ya bada Naira Miliyon uku, dayan kuma ya bada Miliyon biyu, Jimillar kudin ya zama Naira Miliyon Goma.

An Karrama wasu fitattun mutane uku da suka shahara Wajen kokarin bayar da zakkar ga wannan Hukuma, domin nuna gamsuwa tare da jinjinawa kokarin nasu.

Manyan Jami’an Gwamnati, Kalamai da masu yiwa Hukumar da Jihar Kano fatan alhairi be Suka halarci taron da aka gudanar a harabar shelkwatar Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ranar Talatar knowledge Gabata.

What's On Your Mind?