Hukumar Zakka Ta Jihar Kano Ta Fara Raba Shaidar Biyan Zakka

0
102

Hukumar Zakka Ta Jihar Kano Ta Fara Raba Shaidar Biyan Zakka

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Hukumar Zakka da Khubusi ta Jihar Kano a hukumance ta fitar da shaidar yabo  ga wadanda suka biya zakkarsu ta karkashin Hukumar domin zama gamsasshiyar hujjar biyan Zakkar. Da yake mika takardar shaidar  biyan Zakkar ga shugaban Kamfanin Ammasco, Alhaji Muhammad Mustapha  Ado, babban daraktan Hukumar Zakka da Khubusi na JIhar Kano  Alhaji Safiyanu Ibrahim  Abubakar  ya bayyana cewa dalilin  ziyarar tasu shi ne  domin gabatar da shaidar biyan zakkar tare da nuna farin ciki bisa abinda aka baiwa hukumar a matsayin Zakka.
Alhaji Safiyanu Ibrahim Abubakar ya bukaci masu hannu da shuni da sauran kungiyoyi da suyi koyi da abinda shugaban Kamfanin na Ammasco ya yi domin rage matsalar fatara da ta mamaye talakawa da mabukata da kuma masu bukata ta musamman a Jihar Kano.

Daganan sai ya jinjinawa kokarin shugaban Kamfanin tare da  yabawa bisa yadda yake daukar harkokin addinin musulunci da muhimmacin gaske,  inda ya bukaci da ya kara kaimi kan haka ta hanyar  bayar da sadaka ga Hukumar da kuma al’ummar dake zagaye dashi.
Da yake gabatar da jawabinsa, Alhaji Ado ya godewa sarki Allah da ya bashi lafiya da kuma damar shaida wannan rana, yace baya bata lokaci  wajen sauke nauyin abinda addini ya wajabta masa. Shugaban wanda ya yi Magana ta bakin  manajan daraktansa, Alhaji Ibrahim Muhammad Mustapha ya godewa hukumar bisa wannan ziyarar zumunci, ya kuma yi alkawari ci gaba da kiyaye dukkan umarnin Gwamnati.
Wadanda suka raka babban daraktan Hukumar ta Zakka da Khubusi zuwa wurin wannan ziyara, solar hada da daraktan mulki da harkokin yau da kullum, Mustapha Ibrahim Fagge, daraktan shirye shirye, Shehu Muhammad Nata’ala da kuma Darakta PRS Yunusa Harurna  da sauran ma’aikatan hukumar. Kamar yadda mai magana da yawun hukumar Muta’addif Ibrahim Babakaina ya shaidawa MOBILIZED9JA A Yau.

What's On Your Mind?