Hukumar Tace Fina Finai Akwai Aiki Gabanta – Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

0
119

Hukumar Tace Fina Finai Akwai Aiki Gabanta - Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ja hankalin hukumar tace fina-finai ta jihar Kano cewa da ta kara rubanya kokarin ta da ta ke yin a wajen samar da dokokin da za su tsaftace harkar sana’ar fina-finai da gidajen kallo a fadin jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne yayin da jami’an tace fina-finai ta jihar Kano karkashin jagorancin sakataren hukumar, Alhaji Isma’il Muhammad Na Abba Afakallahu ya kai ziyara masarautar Kano.

Wani yawa malamin makaranta yankan Rago a Faransa saboda batanci ga Annabi Muhammad (SAW)

Sarkin ya ce”Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta na da gagarumin aiki a gaban ta na tantance sha’irai da ma su gidanjen kallo a Kano da nufin inganta tarbiyar matasa a jiha baki daya”. Inji Sarkin Kano.

Shi ma a nasa jawabin babban sakataren hukumar, Alhaji Isma’ila Muhammad Na Abba Akafallahu ya ce”Hukumar sa ta yi shirye-shirye, domin kafa kwamiti da zai tantance ma su shirya fina-finai da sha’irai a fadin jihar Kano baki daya”. Inji Afakallahu.

What's On Your Mind?