Hukumar NAFDAC Ta Lalata Miyagun Kwayoyi Na Miliyan 515 A Gombe

- Advertisement -

Hukumar NAFDAC Ta Lalata Miyagun Kwayoyi Na Miliyan 515 A Gombe

Daga Sulaiman Ibrahim

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta kasa reshen jihar Gombe ta lalata miyagun kwayoyi, magunguna marasa inganci, jabu da wadanda suka lalace da darajarsu takai Naira Miliyan 515.

A lokacin da ya halarci kona kayan, babban daraktan hukumar, na yankin Arewa Maso gabas, Farfesa. Mojisola Adeyeye, ya ce hakan yana daga cikin ayyukan hukumar NAFDAC.

Mataimakin daraktan NAFDAC, Josephine Daliyim wanda ya wakilce ta, ya ce magungunan da aka lalata solar hada da magungunan rigakafi, magungunan cutar hawan jini, maganin zazzabin cizon sauro, magungunan yaki da ciwon sukari.

Ta ce sauran kayayyakin da aka lalata solar hada da spaghetti, man girki, abubuwan sha marasa maye, ruwan leda, man shafawa da sinadarai kamar maganin kwari.

- Advertisement -