Hukumar Jami’ar Jihar Kaduna Ta Ninka Kudin Makarantar Sau Shida

0
91

Hukumar Jami’ar Jihar Kaduna Ta Ninka Kudin Makarantar Sau Shida

An ruwaito cewa a baya, sabbin daliban wadanda kuma suke ‘yan asalin jihar Kaduna ne suka biyan kudin makarantar da ya kai naira 23,000 a fannin kwasakwasai, inda kuma a fanin kwas din kimiyya suke biyan naira 27,000, sai kuma dalibai wadanda ba ‘yan jihar ba suna biyan naira 33,000 a sauran kwasakwasai, inda kuma a fanin kwas din kimiyya, suna biyan naira 37,000.

Sai dai, an ruwaito cewa, daga kan sabbin dailbai da suka fara yin rijistar shiga jami’ar, mahukuntan jami’ar solar sake sabunta karbar kudin shiga jami’ar, inda suka ninka har sau shida.

Bugu da kari, dalibai masu karatun kwas din kimiyya a jami’ar wadanda kuma ba ‘yan asalin jihar Kaduna ba, ana sa ran a yanzu, za su biya naira 500,000, inda kuma wadanda suke ‘yan jihar za su biya naira 300,000.

Har ila yau kuma daliban da ba ‘yan jihar Kaduna ba, da suke son karanta kwas din kiwon lafiya da kwas din hada magunguna ana sa ran za su biya naira 300,000, inda kuma dalibai wadanda a ‘yan asalin jihar Kaduna ne, za su biya naira 200,000.

Sace Daliban Jami’a A Kaduna: Yadda ‘Yan Bindiga Suka Shammaci Jami’an Tsaro

Hakazalika, an ruwaito cewa, dalibin da ba ‘yan jihar Kaduna ba, da aka ba su sauran guraben karatun kwasakwasan Kimiyya a jimi’ar, ana sa ran za su biya kudin makaranta naira 220,000, inda kuma dalibai wadanda a suke ‘yan asalin jihar Kaduna ne za su biya naira 170,000.

Har ila yau kuma, daliban da ba ‘yan jihar ta Kaduna bane, aka kuma ba su guraben yin karatu a sauran kwasakwasai, har da na kwas din ilimi da sauransu, ana sa ran za su bya kudin makaranta naira 200,000, inda kuma dalibai wadanda suke yan asalin jihar Kaduna ne za su biya naira 150,000.

Daya daga cikin daliban dake a matakin karatu na 500 a jami’ar ta KASU mai suna Abdullahi Yakubu Isa ya bayyana cewa, hankula solar tashi matuka a jami’a, musamman ganin cewa, dalban da suka dawo cikin jami’ar solar firgita da jin sabon karin kudin makarantar ganin cewa, hakan zai iya shafarsu.

Abdullahi Yakubu Isa wanda kuma shi ne kakakin yada labarai na kungiyar dalibai na jami’ar ya ci gaba da cewa, “ A yanzu muna kan tuntuba, domin yanayi a jami’ar yanzu ya ana kara dumamar”.

A cewar Abdullahi Yakubu Isa, daliban da suka saba biyan kudin makaranta sama da naira 23, 000, amma kawai su wayi gari sunji cewa, an kara kudin makarantar zuwa sama da naira 200,000, wannan babbar matsala ce kuma dalibai da dama na jami’ar solar shiga cikin rudani da damuwa.

Abdullahi Yakubu Isa ya bayyana cewa, mahukuntan jami’ar solar gaza wajen sabunta tsarin, inda ya yi nuni da cewa, hakan zai janyo daliban jami’ar da dama su ba su da wani zabi, illa su jingine ci gaba da yin karatunsu.

An yi kokarin jin ta bakin mahukuntan jami’ar don jin ta bakinsu kan lamarin, amma hakan ya ci tura duk da alkawarin da Kakakin yada labarai na jami’ar Adamu Bargo ganinsa ya faskara .

Bugu da kari, an kuma je ofishinsa a jiya Alhamis domin karin bayani, amma ance yana halartar wata ganawa .

What's On Your Mind?