Hukumar ITF Ta Samar Wa Matasa 4,500 Sana’o’in Dogaro Da Kai A Sakkwato

- Advertisement -

Hukumar ITF Ta Samar Wa Matasa 4,500 Sana’o’in Dogaro Da Kai A Sakkwato

Daga Bello Hamza, Abuja

Matasa fiye da four,500 suka samu horon sana’o’in dogaro da kai daga hukumar ITF a jihar Sakkwato.

Shugaban hukumar, Sir Joseph Ari, ya bayyana haka a taron rufe shirin horas da matasan a garin Sakkwato ranar Laraba.

Shugaban wanda shugaban hukumar na yankin Sakkwato, Mr Dauda Mshelizah, ya wakilta, ya ce, hukumar ta samu nasarar horas da matasa da dama a fadin tarayyar kasar nan tun da aka fara gudanar da shirin a shekarar 2013.

Ya ce, an kirkiro da shirin ne don ya karfafawa gwamnatin tarayya a kokarinta na samarwa matasa ayyukan yi don su zama masu dogaro da kansu.

Ya kuma ce, an horas da matasa 105 sanar dinki da kuma na aiki da naura mai kwakwalwa.

Akan haka ya bukaci matasa su yi amfani da shirin horaswar don bunkasa rayuwarsu, Su kuma godewa shugaban kasa Muhammad Buhari akan yadda ya samar da shirin.

A jawabinsa, sakataren gwamnatin Jihar, Alhaji Sa’idu Umar, ya yaba wa hukumar akan kokarin su na horas da matasa, ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta cigaba da bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata don kara bunkasa shirin a fadin Jihar.

Wasu da suka amfana da shirin, Marliyya Ahmad, Jamilu Umar da Shehu Bello solar mika godiyarsu akan horaswar da aka yi musu solar kuma ce lallai shirin zai bunkasa rayuwarsu.

- Advertisement -