Hukumar EFCC ta sa an Yankewa Wani Mutumi hukuncin Daurin Shekaru fiye da 100

0
51

Wata babban kotun jihar Borno da ke zama a garin Maiduguri, ta yankewa wani mutumi mai suna Allen Abel, dogon dauri a gidan kurkuku.

Mista Allen Abel zai shafe shekaru 125 a gidan maza bayan kotu ta identical shi da laifin karbar kwangilar karya na kawo kayan abinci.

The ICIR ta ce wannan mutumi ya karbi kwangilar karya ta cewa zai shigo da buhunan shinkafa da kwalayen taliya har na N12, 879,800.

Hukumar EFCC ta sa an Yankewa Wani Mutumi hukuncin Daurin Shekaru fiye da 100

Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya shaidawa ICIR wannan jiya.

Wannan mutumi ya karbo kwangilar karyar ne da sunan ma’aikatar bada tallafi da agajin gaggawa a karkashin tsarin ciyar da ‘yan makaranta.

EFCC ta gurfanar da Abel a gaban Alkali mai shari’a, Aisha Kumaliya tare da wasu; Suleiman Adamu, Usman Adamu da Kingsley Madubuagu.

Zargi 20 da ake yi wa Abel da sauran mutane uku solar hada da mallakar takardun karya da kuma amfani da sunan wani ta hanyar shaidar karya.

Fyade: Kotu ta Kori Soja Daga Aiki, ta Yanke Masa Hukuncin Shekaru 5 a Gidan Yari

Mai magana a madadin EFCC ya ce an samu Abel da laifin karbar kwangilar karya ta buhuna 480 na shinkafa da kwalaye 1313 na taliya a kan miliyan 12.

Wannan mutumi ya karbi kayan abincin ne daga Lelle Hyelwa Sini na kamfanin Lelle Foresight Building Co. Ltd da sunan gwamnatin tarayya.

A karshe an yankewa Abel daurin shekaru bakwai, biyar, biyar da sauransu. Kuma zai biya kamfaonin Lele Foresight da Lele Foresight kudinsu.

Idan za ku iya tunawa, a shekarar nan ne Kotu ta yankewa tsohon kakakin PDP na kasa, Olisah Metuh hukuncin daurin shekaru 39 a gidan yari.

Alkali Okon Abang ya zartar da hukuncin a kan Metuh bayan an identical shi da laifin almundahana.

What's On Your Mind?