Hukumar DSS ta zagaye gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

0
84

An ga jami’an tsaro masu yawa a kusa da gidan Sheikh Abdujabbar Nasiru Kabara a Gwale da ke karamar hukumar Gwale a cikin garin Kano.

Jaridar Legit hausa ta ruwaito cewa a safiyar yau Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakatar da shahararren malamin addinin Islama din daga yin wa’azi a jihar saboda salon koyarwarsa da ake ganin yana da matukar tsanani.

Gwamnatin jihar ta kuma bayar da umarnin cewa a rufe dukkan makarantun da malamin ke gudanarwa har sai hukumomin tsaro solar gudanar da bincike.

Hukumar DSS ta zagaye gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Martanin Da Malaman Kano Sukayiwa Abduljabbar A Gaban Gwamna Ganduje

Rahoto ya lura da kimanin motoci biyar na jami’an tsaro masu dauke da manyan makamai, tun daga ‘yan sanda zuwa DSS, da jami’an tsaro na NSCDC da sauran wadanda suka kewaye gidan don tabbatar da bin da dokar da aka kafa wa malamin.

Su, duk da haka, basu hana mabiya da masu yi masa jaje shiga gidan ba.

An ga daruruwan mabiya a kewayen gidan da harabar masallacin malamin suna jimami kan matakin Gwamnatin Jihar.

Sheikh Abduljabbar, mabiyin darikar Qadiriyya, ana ganin ya samu sabani tsakanin manyan malamai a jihar.

What's On Your Mind?